Home Back

Man United na son Zirkzee, watakila Joselu ya bar Real Madrid

bbc.com 2024/8/21

Asalin hoton, Getty Images

.
Bayanan hoto, Joshua Zirkzee

Ana sa ran Manchester United za ta amince da biyan kusan fam miliyan 40, domin siyan dan wasan gaba na Netherlands, mai taka leda a Bologna Joshua Zirkzee, 23, suna kuma tattaunawa da Lille, kan dan wasan Faransa Leny Yoro, mai shekara 18.(Sky ports),

United na fatan siyan Zirkzee, idan ta sayar da dan wasan tsakiya na Ingila Mason Greenwood, mai shekara 22. (I Sport)

Everton ma na fatan Manchester United, ta sayi mai tsaron baya na Ingila, Jarrad Branthwaite, mai shekara 18. (Liverpool Echo)

Everton din dai na gab da kammala yarjejeniyar siyan dan wasan gaba na Senegal Iliman Ndiaye, mai shekara 21 daga Marseille. (Footmercato - in French)

Manchester United na fatan sake sabon kwantiragi da Erik ten Hag, kafin a fara rangadin shirin sabuwar kakar wasa zuwa Amurka, a watan gobe. (ESPN)

Tsohon dan wasan Manchester United, Van Nistelrooy, mai shekara 47, sun yi tattaunawa mai armashi kan batun komawarsa kungiyar a cikin shirin horas da 'yan wasa da Ten Hag ke yi. (Talksport)

Dan wasan gaba na Sifaniya Joselu, 34, na gab da barin kungiyar Real Madrid, bayan da ya samu tayi mai gwabi daga kulub din Al Gharafa, na kasar Qatar. (Athletic - subscription required)

Chelsea ta fara tattaunawa da Barcelona, kan dan wasan gaba na Sifaniya, Marc Guiu, mai shekara 18. (ESPN)

Chelsea dai ta yi wa Bayern Munich, fintinkau kan siyan Guiu, da ita ma ke muradi. (Fabrizio Romano)

People are also reading