Home Back

Ganduje: Shugaban APC Na Tsaka Mai Wuya Yayin da Aka Sake Maka Shi a Kotu

legit.ng 2024/7/4
  • Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje na ci gaba da fuskantar matsin lamba yayin da aka sake maka shi a gaban kotu
  • Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ce za ta fara sauraron gundarin karar da aka nemi sauke Ganduje daga shugabancin APC
  • Ƙungiyar mambobin APC na shiyyar Arewa ta Tsakiya ce ta shigar ƙarar domin neman a dawo ma yankin da haƙƙinsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja za ta fara zaman sauraron ƙorafin da aka nemi ta sauke shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dokta Abdullahi Umar Ganduje.

Mai shari'a Inyang Ekwo ne ya sanya ranar fara sauraron ƙarar bayan lauyan masu ƙara, Benjamin Davou, ya roƙi kotu ta sanya lokacin fara zama kan shari'ar.

Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje.
Kotu ta zabi ranar fara zaman shari'a kan kujerar shugaban APC na kasa Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje Asali: Twitter

Ƙungiyar magoya bayan APC a shiyyar Arewa ta Tsakiya karkashin jagorancin Saleh Zazzaga ce ta maka Ganduje a kotu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta tuhumi yadda ana naɗa Ganduje a matsyain shugaban jam'iyya mai mulki duk da shi ba ɗan shiyyar Arewa ta Tsakiya ba ne.

Waɗanda ake tuhuma a ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/599/2024 sun haɗa da Ganduje, jam'iyyar APC da hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC).

Yayin da aka dawo zama kan karar jiya Alhamis, Davou ya ce duk da cewa an shirya sauraron shari'ar, amma ba zai yiwu ba saboda lauyan Ganduje, Raymond Asikeni, ya yanki hanzari.

Lauyan shugaban jam'iyya ya shigar da ƙorafin cikin shari'a inda ya nuna sam bai aminta da wannan ƙara ba.

Amma Davou ya yi alkawarin zai mayar da martani ga takardun da Ganduje ya gabatar a ranar Laraba bayan hutun babbar Sallah.

Daga nan sai mai shari’a Ekwo ya dage zaman zuwa ranar 26 ga watan Yuni, 2024 domin fara shari'ar gadan-gadan.

"Idan aka dawo zaman shari'a, kotu za ta sauraro ƙorafin farko da kuma gundarin shari'ar," in ji alkalin.

APC ta soki Atiku da PDP

A wani rahoton kun ji cewa APC mai mulki a Najeriya ba ta ji daɗin kalaman da Atiku Abubakar da jam'iyyarsa ta PDP suka yi ba kan Bola Ahmed Tinubu.

Jam'iyya mai mulki ta bayyana cewa ba daidai ba ne ɗora alhakin halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan kan Shugaba Tinubu.

Asali: Legit.ng

People are also reading