Home Back

Za a Sha Jar Miya: Tinubu Zai Fara Biyan Tallafin N150bn Ga ’Yan Kasa, Jama’a Za Su Caba

legit.ng 4 days ago
  • Gwamnatin Tarayya ta fadi ranar fara biyan tallafin bashi har N150bn ga masu kananan sana'o'i da 'yan kasuwa
  • Ministar masana'antu da kasuwaci, Doris Uzoka-Anite ta tabbatar da cewa a karshen watan Yulin 2024 za a fara biya
  • Ministar ta kuma yi godiya ga wadanda suka cike neman tallafin inda ta yaba musu kan hakurin da suka nuna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sanya ranar raba bashin N150bn ga kananan 'yan kasuwa da masu sana'o'i.

Gwamnatin Bola Tinubu ta bayyana haka ne a jiya Alhamis 27 ga watan Yunin 2024 a birnin Tarayya Abuja.

Tinubu ya shirya biyan tallafin N150bn ga 'yan Najeriya
Bola Tinubu ya shirya fara biyan tallafin N150bn a karshen watan Yulin 2024. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu. Asali: Facebook

Tinubu ya shirya biyan tallafin N150bn

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ministar masana'antu da kasuwanci, Doris Uzoka-Anite ita ta tabbatar a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uzoka-Anite ta tabbatar da cewa zuwa karshen watan Yulin 2024 za a fara biyan kudin ga wadanda suka cika ka'ida.

Ta ce 60% na kudin an raba su ga 'yan kasar inda suka samu N50,000 a kananan hukumomi 774 na kasar kyauta ba bashi ba.

A watan Disambar 2023 ne Tinubu ya kaddamar da tallafin domin taimakawa masu kananan sana'o'i da 'yan kasuwa.

Yadda Tinubu ya kasafta kudin tallafin

Daga cikin kudin da aka ware na N150bn, an tura N75bn ga masu kananan sana'o'i da kuma N75bn ga masana'antu.

Ministar ta ce gwamnati ta san halin da tattalin arzikin ke ciki shi yasa ma ta ware kudin domin shawo kan matsalolin da ake ciki.

"Wadanda suka cike talafin nan har yanzu ba mu biya ba, muna kara gode muku kan irin hakuri da kuke yi."
"Ana ci gaba da biya saboda mun ware 60% na kudin a kananan hukumomi 774 da muke da su."
"Kowa zai iya bibiyar wadanda suka ci gajiyar a kananan hukumomi ta wannan yanar gizo: grant.fedgrantandloan.gov.ng/learning/dis."

Tinubu zai kuma ba da sabon tallafi

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da tallafawa gidaje miliyan 3.6 a yankunan Najeriya guda shida.

Tinubu ya tabbatar da cewa akalla gidaje akalla N50,000 ne zuwa N100,000 za su samu wannan tallafi na tsawon watanni uku.

Asali: Legit.ng

People are also reading