Home Back

Gwamnatin Sakkwato Na Ci Gaba Da Shirin Tsige Sarkin Musulmi – MURIC

leadership.ng 2024/7/3
Gwamnatin Sakkwato Na Ci Gaba Da Shirin Tsige Sarkin Musulmi – MURIC

Duk da cewa gwamnatin Jihar Sakkwato ta musanta shirin tsige Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC), ta ce har yanzu gwamnatin na ci gaba da shirin tsige Sarkin.  

Farfesa Ishaq Akintola, Babban Daraktan MURIC ne, ya bayyana hakan, inda ya yi nuni da kudurin dokar gyara masarautun jihar, wadda ta tsallake karatu na daya da na biyu a majalisar dokokin jihar a ranar Talata.

Idan har aka zartar da kudurin dokar za ta hana Sarkin Musulmi daga yin nadin manyan mukamai da suka hada da nada sarakuna da hakimai ba tare da amincewar gwamnati ba.

Akintola ya yi Allah-wadai da gyaran, inda ya bayyana shi a matsayin wani yunkuri na kawo cikas ga Sarkin Musulmi da kuma rage masa kima.

Ya bayar da shawarar cewa gwamnan ya shimfida harsashin ruguza Majalisar Sarkin Musulmi.

Hakan ya biyo bayan tsige sarakunan gargajiya 15 da gwamnan ya yi a baya-bayan, lamarin da Akintola ke kallonsa a matsayin wata alama ta mulkin kama-karya da kuma yunkurin mayar da lamarin siyasa.

MURIC ta yi kira da a gudanar da bincike kan dalilin tsige sarakunan.

Akintola ya bukaci ‘yan majalisar dokokin Sakkwato da su fahimci muhimmancin Majalisar Sarkin Musulmi ga sauran daukacin al’ummar Najeriya.

Ya yi gargadin cewa abubuwan da ake yi a halin yanzu na iya haifar da rashin zaman lafiya da rudani ba a iya jihar ba har ma da Najeriya.

People are also reading