Home Back

Abuja: Tashin Hankali Yayin da Wani Abu da Ake Zargin 'Bam' Ne Ya Tashi da Mutane a Watan Azumi

legit.ng 2024/5/9
  • Mutane sun shiga fargaba yayin da wani abu da ake zargin bam ne ya tashi a birnin tarayya Abuja ranar Jumu'a
  • Mazauna yankin sun ce abun ya fashe ne a ɗakin wasu mutum biyu maza, sun ce tukunyar gas ce amma babu wata alamar hakan
  • A cewar wata majiya, sun kai rahoton lamarin ga ƴan sanda kuma akwai bukatar dakarun kwance bama-bamai su halarci wurin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - An shiga tashin hankali da fargaba a wasu sassan birnin tarayya Abuja, sakamakon fashewar wani abu a ranar Juma'a, 29 ga watan Maris, 2024.

An tattaro cewa mutum daya ya samu raunuka yayin da wani abu ya fashe a yankin Dawaki da ke ƙaramar hukumar Bwari a birnin Abuja.

Sufetan ƴan sanda, IGP Kayode.
Wani abu da ba a san menene ba ya fashe a Abuja Hoto: PoliceNG Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar The Nation ta tattaro, lamarin ya faru ne da safiyar ranar Jumu'a yayin da musulmi ke ci gaba da azumin watan Ramadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗaya daga cikin mazauna yankin ya shaidawa manema labarai cewa sun ji wata ƙara mai ƙarfi a wani gida mai daki daya dauke da maza biyu.

Menene abin da ya fashe a Abuja?

Duk da wani mazaunin yankin ya ce ana zargin tukunyar gas da ake girki da ita ce ta fashe amma har yanzun ba su ji warin gas a wurin ba, rahoton Sahara Reporters.

Mutumin ya ce:

"Mun ji ƙara mai ƙarfi a nan cikin Dawaki, karar ta taso ne daga wani gida mai ɗaki ɗaya wanda wasu maza biyu ke zaune a ciki, mutum ɗaya daga cikinsu ya samu rauni kuma an kwantar da shi a asibiti.
"Abokin zamansa ya faɗa mana yana tsammanin tukunyar gas ce ta fashe, amma ba mu ji warin gas ba, babu wuta kuma tagar kicin ta karye yayin da sauran tagogin falon suka lalace.
"Tuni dai lamarin ya shiga hannun ƴan sandan Dawaki, amma ina ganin ya kamata dakarun kwance bama-bamai su ziyarci wurin domin gano haƙiƙanin abin da ya fashe tun wuri."

Duk wani kokarin jin ta bakin jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan FCT, Josephine Adeh ya ci tura domin ba ta daga kiran waya ko amsa sakon tes.

Ƴan sanda sun mika sarkin Ikolo ga sojoji

A wani rahoton kuma Yan sanda sun miƙa Sarkin Ewu, Clement Ikolo, ga rundunar sojoji bayan ya miƙa kansa da yammacin ranar Alhamis

Basaraken na ɗaya daga cikin mutum 8 da hedkwatar tsaron Najeriya take nema kan zargin hannu a kisan gillan da aka yi wa sojoji 17 a Okuama

Asali: Legit.ng

People are also reading