Home Back

Barazanar Alakar Jinsi: Abubuwa 10 da Ba a Sani Ba Game da Kundin Yarjejeniyar Samoa

legit.ng 2024/10/6
  • A makon da ya wuce ne aka rika ce-ce-ku-ce a kan yarjejeniyar Samoa da gwamnatin tarayyar Najeriya ta rattabawa hannu
  • Yan Najeriya da dama sun koka bayan jin cewa yarjejeniyar ta ƙunshi ba yan luwadi da madigo cin karensu ba babbaka
  • A kan haka ne Legit ta tattaro muku abubuwa guda 10 da za su wayar da kan al'umma kan abin da yarjejeniyar Samoa ta kunsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Al'ummar Najeriya sun dauki zafi bayan tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta saka hannu kan yarjejeniyar Samoa.

Hakan ya biyo bayan jin kishin kishin din cewa yarjejeniyar za ta ba masu luwadi da madigo kariya duk da kokarin gwamnati na fayyace gaskiyar lamarin.

Yarjejeniyar Samoa
Abubuwa masu muhimmaci kan yarjejeniyar Samoa. Hoto: Rabyn Hock Asali: Getty Images

A wani bincike da jaridar Punch ta yi, ta fitar da abubuwa guda 10 domin wayar da al'umma kan yarjejeniyar Samoa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwa 10 kan kundin yarjejeniyar Samoa

  1. Yarjejeniyar Samoa an yi ta ne tsakanin kasashen Turai da ƙasashen OACPS wanda suka kunshi kasashen Afrika.
  2. Ana kiran yarjejeniyar da 'Yarjejeniyar Samoa' ne kasancewar an rattaba mata hannu ne a kasar Samoa.
  3. Yarjejeniyar ta ƙunshi muhimman abubuwan ne guda shida domin magance matsalolin kasashen da suka rattaba hannu a cikin shekaru 20.
  4. Ambasadan Najeriya a kasar Baljiya, Obinna Onowu ne ya rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin Najeriya a ranar 28 ga watan Yuni.
  5. Muhimman abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa sun hada da yancin dan Adam, tabbatar da dimokuraɗiyya, samar tsaro da zaman lafiya, cigaban ƙasa, rashin nuna wariya, haɓaka tattali.
  6. Yarjejeniyar ta yarda ga kasashe su dauki matakin da ya dace da yanki, kasa ko garin da suke rayuwa.
  7. Ba a samu sashin da yake magana a kan amincewa da madigo ko luwadi a cikin yarjejeniyar kai tsaye ba.
  8. Kasashen Turai sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tun ranar 15 ga watan Nuwambar shekarar 2023.
  9. Ana hasashen cewa yarjejeniyar za ta kara karfin alakar Najeriya da kasashen Turai wajen samun tallafi da sauransu.
  10. Dole sai majalisar zartarwa, majalisar tattalin Najeriya da majalisar ƙasa sun amince da yarjejeniyar kafin ta tabbata a Najeriya.

Sheikh Jingir ya yi magana kan Samoa

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake cece-kuce kan yarjejeniyar Samoa, Sheikh Sani Yahaya Jingir a ya bayyana matsayarsa kan lamarin.

Sheikh Jingir ya yi fatali da yarjejeniya inda ya ce da Musulmi da Kirista da sauran masu addinai duk sun ce ba za su goyi bayan wannan ba.

Asali: Legit.ng

People are also reading