Home Back

ZARGIN HARƘALLAR MUGGAN ƘWAYOYI: Kotu ta yi watsi da neman belin Abba Kyari

premiumtimesng.com 2024/7/1
KYARI YA ƁALLO RUWA: ‘Yadda jami’an NDLEA ke taimakon masu shigo da muggan ƙwayoyi cikin Najeriya -Inji Kyari

Bayan Babbar Kotun Tarayya ta bada belin Abba Kyari cikin watan jiya, tsawon makonni biyu domin ya halarci zaman makokin rasuwar mahaifiyar sa, a wannan karo kuma kotun ta hana belin sa a ranar Laraba, shi da wasu jami’an ‘yan sanda huɗu da ake tuhuma da laifin safarar muggan ƙwayoyi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Mai Shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya, ya ce waɗanda ake tuhumar ba su gabatar wa kotun gamsassun dalilan da za a iya bada belin su ba.

Nwete ya ce kotu ce ke da ikon bada belin wanda ake tuhuma, kuma tilas bayar da wannan beli sai an bi ƙa’idojin da doka ta tanadar.

Idan za a iya tunawa, PREMIUM TIMES Hausa ta buga labari a cikin watan Mayu, inda kotu ta bada belin Abba Kyari, tsawon makonni biyu domin ya halarci jana’iza da zaman-makokin mahaifiyar sa.

A wancan lokacin, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bada belin tsohon Kwamandan Rundunar ‘Yan Sandan IRT, Abba Kyari na tsawon kwanaki 14, domin ya je gida Jihar Barno ya halarci jana’iza da zaman-makokin mahaifiyar sa.

An bada belin Abba Kyari bayan ya shafe fiye da shekaru biyu a tsare. Kyari da sauran abokan aikin sa da ke tsare, su na fuskantar tuhumar haɗin-baki wajen safarar hodar Iblis da ƙoƙarin kare mai laifi.

Mai Shari’a Emeka Nwite ya hana bada Kyari beli har sau biyu a baya, bisa dalilin cewa shi da sauran waɗanda ake tuhuma ɗin sun kasa bada dalilin beli mai gamsarwa.

Amma a ranar Talata, kotu ta bada belin Kyari domin ya je gida ya halarci jana’izar mahaifiyar sa a Jihar Barno.

Mai Shari’a ya ce a fitar da Kyari daga Gidan Kurkukun Kuje inda ya ke tsare ya je gida, amma kada ya wuce makonni biyu.

Sauran waɗanda ake tuhuma tare da Kyari sun haɗa Sunday Ubua, Bawa James, Simon Agirgba da John Nuhu, waɗanda dukkan su ‘yan sanda ne masu muƙamai daban-daban.

Akwai kuma fararen hula biyu, Chibunna Umeibe da Emek Ezenwanne.

People are also reading