Home Back

Manchester United ta tsawaita kwataragin Ten Hag

bbc.com 4 days ago
A

Asalin hoton, Getty Images

Kocin Mnchester United Erik ten Hag ya tsawaita kwantaraginsa a kungiyar da shekara guda, zai ci gaba da zama a ƙungiyar zuwa 2026.

Dan ƙasar Netherlands din da aka ɗauka a 2022 an tsara kwantaraginsa za ta ƙare ne a 2025.

Ten Hag wanda ya koma United daga Ajax, ya lashe kofuna biyu a zamansa na Old Trafford a shekara biyu.

"Na ji dadin daidaitawar da muka yi da ƙungiyar da za mu ci gaba da aiki tare," in ji mai shekara 54.

"Idan muka duba shekara biyu baya, za mu yi alfahari da nasarar da muka samu ta lashe kofuna biyu, da kuma ci gaban da muka samu a kungiyar daga inda muka same ta."

Ten Hag ya ce "dole mu amince da cewa akwai karin aiki mai yawa a gabanmu".

A kakar farko da Ten Hag ya zo United ya kammala Premier a matsayi na uku, yayin nasarar da kungiyar ya samu ta lashe Carabao ya kawo karshen zaman United na shekara shida ba tare da cin kofi ba.

Amma kaka ta biyu ta kocin ta kasance mai wuya, saboda ya kammala kakar a matsayi na takwas an kuma cire shi daga gasar Champions a matakin rukuni.

Nasarar da ya samu da ci 2-1 kan Manchester City a gasar FA ta ba shi damar ci gaba da zama a kungiyar.

People are also reading