Home Back

Aikin Bututun Gas Na AKK Zai Bunƙasa Tattalin Arziƙin Arewacin Nijeriya – Minista

leadership.ng 6 days ago
Aikin Bututun Gas Na AKK Zai Bunƙasa Tattalin Arziƙin Arewacin Nijeriya – Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce aikin shimfiɗa bututun gas daga Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK) zai bunƙasa hanyoyin tattalin arzikin Arewacin Nijeriya.

A takardar sanarwa ga manema labarai da ya rattaba wa hannu, mai ba ministan shawara kan aikin jarida, Malam Rabiu Ibrahim, ya ce, Idris ya bayyana haka ne a Kaduna a lokacin da ya kai ziyara wurin aikin bututun gas na AKK da ake yi a gaɓar Kogin Kaduna.

Ya halarci wurin ne tare da rakiyar Ministan Kuɗi, Wale Edun; da Ƙaramin Ministan Albarkatun Gas, Mista Ekperikpe Ekpo, da kuma Shugaban Kamfanin NNPC, Mele Kyari.

A jawabinsa a wajen ziyarar, Idris ya ce, “Aikin na AKK ya mayar da hankali ne wajen fitar da ɗimbin ƙarfin tattalin arzikin Arewacin Nijeriya. Gas ɗin da za a yi jigilarsa zai samar da makamashin da ake buƙata ga gidaje, kasuwanci, da masana’antu, sannan kuma zai ba da damar hada-hadar sufuri da rage farashin sa.

“Ci gaba da aiwatar da wannan aiki, wanda shi ne babban aikin bututun gas na cikin gida a Nijeriya zuwa yanzu, wanda gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta yi, wata alama ce da ke nuni da ƙudirin Shugaban Ƙasa na bunƙasa masana’antu da ci gaban tattalin arzikin kowane ɓangare na ƙasar nan.”

Haka kuma ya yaba da aikin a matsayin mai muhimmanci ga cigaban masana’antu da tattalin arzikin Nijeriya a ƙarƙashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana shi a matsayin aikin bututun gas na cikin gida mafi girma a ƙasar.

Ministan ya kuma danganta cigaban tattalin arziki da tsaro, inda ya ce yawancin matsalolin tsaro da ake fama da su a Arewacin Nijeriya suna faruwa ne sakamakon taɓarɓarewar tattalin arziki, wanda za a iya ragewa ta hanyar samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziƙi.

Ya ce, “Samar da makamashi a gidaje, gonaki, da masana’antu ya na da matuƙar muhimmanci ga samar da ayyukan yi masu yawa.”

Idris ya bayyana yiwuwar aikin zai taimaka wa harkar noma sosai a Arewacin Nijeriya.

Bugu da ƙari, ya yi nuni da irin tasirin da irin waɗannan ayyuka ke yi a faɗin ƙasar nan, inda ya ce a watan da ya gabata an ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan samar da gas guda uku a yankin Neja Delta.

Ya ƙara da cewa aikin na AKK zai tallafa wa Shirin Shugaban Ƙasa na Gas (Pi-CNG), wanda tuni ya jawo jarin sama da dalar Amurka miliyan 50.

Ya ce, “Aikin bututun na AKK wani ginshiƙin fata ne, wanda zai farfaɗo da tattalin arzikin dukkan ‘yan Nijeriya.”

People are also reading