Home Back

Sallah Ƙarama: Abun Da Ya Kamata Ku Sani Kan Sallar Idi Da Ladubanta

leadership.ng 2024/5/13
Sallah Ƙarama: Abun Da Ya Kamata Ku Sani Kan Sallar Idi Da Ladubanta

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Yabo da godiya da kirari da girmamawa sun tabbata ga Allah shi kaɗai. Yabon Allah da amincinsa su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta shugaban farko da na ƙarshe tare alayensa da sahabbansa baki ɗaya.

Bayan haka; wannan rubutu ya ƙunshi bayani a kan sallar idi a bisa fahimtar Mazhabar Malikiyya. Ga bayanin kamar haka.

1. Sallar idi sunna ce mai ƙarfi ta wajibi.

2. Liman da mamu za su tafi filin idi bayan rana ta fito domin suna isa filin idi hantsi ya yi sai a yi sallah.

3. Ana yin sallar idi a filin idi ba a masallaci ba, sai dai idan akwai lalura, to za a iya yi a masallaci, haka nan waɗanda suke a garin Makka za su yinta a Harami.

4. Mustahabbi ne mutum ya yi wanka domin sallar idi.

5. Mustahabbi ne idan an yi wankan a tafi masallaci ba tare da ɓata lokaci ba.

6. Mustahabbi ne a yi ado a sanya turare da sababbin tufafi ga wanda yake da iko.

7. Za a tafi filin idi ana kabarbari a bayyane har a je filin idi, idan an je ba a yin nafila, za a zauna a ci gaba da kabarbari har liman ya ƙaraso, sai a tsaya da kabarbari. Idan liman yana kabarbari, nan ma mamu za su yi kabarbari idan liman ya yi.

TAMBIHI: Kabarbari aka fi buƙata sama da wa’azi kafin liman ya zo, don Allah a bar al’umma su raya kabarbarbari a wurin idi.

8. Sallar idi raka’a 2 ce , kuma ana yin karatu a bayyane, a raka’a ta farko ana yin kabbara bakwai har da kabbarar harama sai liman ya fara karatu, a ta biyu kuma kabbara shida har da ta mikewa. Ana karanta Fatiha da Sabbi a rakar farko, a ta biyu kuma Hal’ataka ko kuma makamantansu.

9. Idan mutum bai riski wani abu tare da liman ba a raka’a ba, to, zai yi kabbara bakwai a raka’a ta farko kafin ya yi karatu, kuma zai kabbara shida a raka’a ta biyu kafin ya fara karatu kamar yadda liman ya yi.

10. Ba a yin nafila bayan an gama sallar idi.

11. Liman zai yi huɗuba guda biyu kuma zai zauna a tsakaninsu kuma ana so ya yawaita kabarbari a huɗubarsa.

12. Ana so a yi sallar layya da wuri a kan ta sallar azumi, domin ana so a ci abinci kafin a tafi karamar salla, ita kuma ta layya sai bayan an dawo.

13. Kabarbari da ake so a yi, laffuzansu suna da yawa kuma za a iya yin kowanne, daga ciki akwai: Allahu Akbar Allahu Akbar La’ilaha illallahu Allahu Akbar Allahu Akbar Walillahil Hamdu.

14. Ana so a rinƙa kabarbari a bayan kowacce sallar farilla sau uku har zuwa bayan salla da kwana uku, kuma ana so a yawaita zikiri a cikinsu.

15. Mustahabbi ne ga mata da yara idan ba za su je sallar idi ba, to su yi wanka da ado da sanya sababbun kaya idan da hali.

16. Mata su guji caba ado da sanya turare idan za su je idi saboda gudun fitina.

17. Makruhi ne mutum ya ƙi yin ado da kwalliyya da gayu a ranar idi wai don gudun duniya, idan kuma ya ƙi yi da sunan addini, to ya zama ɗan bidi’a.

18. Yara da mata za su iya yin wasanni a ranakun idi.

19. Mustahabbi ne mutum ya sabunta hanya wajen dawo wa gida daga idi, wato ya sauya hanya.

Allah ya karɓa mana ibadunmu, ya gafarta mana. Amin.

Manazarta:

1~ Muwadda Maliki [shafi 87-90] bugun Mu’assatul mukhtar.
2~ al-Mudauwanatul Kubra [1/223-231] ta Imam Malik Riwayatu Imam Hasnun, bugun Maktabatus Sakafati Addiniyyati.
3~ ar-Risãlatu [shafi na 71-72] na Abu Zaid al-Ƙairawãnī,bugun Dãrul Fadīlati.4~ at-Talƙīnu [shafi na 115-116] na Abdulwahab Albagdadi, bugun Dãrul Fadīlati.

5~ al-Ma’ūnatu [1/233-237] na Abdulwahab Albagdadi,  bugun Dãrul Fadīlati.
6~ al-Kãfi [shafi na 128-129] na ibnu Abdilbarri,  bugun Assahwatu.
7~ Mukhtasul Khalil [shafi na 87] na Shehu Khalil, bugun Dãru Ibnil Jauzī.
8~ Sharhul Iziyyati [shafi na 103-106] na Sharnūbi.

9~ Fathu Rabbil Bariyyati [shafi n 558-566] na Masur Sokoto, bugun Maktabatul Imamil Bukhari.
10~ Sirãjus Sãliki [1/135-137] na al-Ujali, bugun Dãrul Fikr11~ Bulgatus Sãliki [1/175-177] na Ahmad as-Sãwi, bugun Dãrul Fikr

13. Assharhu Assagir [1/652-660] na Ahmad ad-Dardir, bugun Dãrul Fadīlati.

14~ Taƙribul Murãdi [shafi na 124-128] na Sulaiman Zamfara, bugun Dãrul Ummati.

15. Jawãhirul Iklil [1/101-104] na Saleh Abdussami’i, bugun Sharikatul-ƙudsi.

People are also reading