Falasdinawa Na Komawa Khan Younis Yayin Da Isra’ila Ta Janye Dakarunta
Falasdinawa sun fara komawa gidajensu da yaki ya rugurguza a Birnin Khan Younis da ke gabashin Gaza bayan da dakarun Isra’ila suka janye daga yankin.
Farmakin da sojojin Isra’ila suka kai ta kasa ya dagargaza gine-ginen yankin.
Ministan tsaron Isra’ila ya ce sojojin sun bar yankin ne domin sake dauro sabuwar damarar yakar Hamas a Khan Younis din da Rafah, inda Falasdinawa sama da miliyan ke gudun hijira.