Home Back

Kamfanin ByteDance ya musanta aniyar sayar da TikTok

dw.com 2024/5/18
Tambarin TikTok
Tambarin TikTok

Kamfanin ByteDance wanda ya mallaki TikTok ya musanta aniyar cefanar da manhajar a Amurka bayan shugaba Joe Biden ya sanya hannu kan dokar da za ta iya haramta amfani da TikTok idan bai nesanta kansa da kamfanin na China ba.


Dambarwar ta TikTok na ci gaba da tada jijiyoyin wuya tsakanin Beijing da Washington.


A yayin wata ziyara da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kai a China ranar Juma'a, ministan harkokin kasashen waje na kasar Wang Yi, ya yi gargadin samun karuwar dalilai marasa dadi da ke shafar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Mr. Yi ya kuma yi ikirarin ana take yunkurin China na neman gina kanta ba tare da wani daliliba. 

People are also reading