Home Back

Majalisar Kano Ta Rusa Sarakunan da Ganduje Ya Kirkiro

legit.ng 2024/6/25

A karshe, Majalisar jihar Kano ta rushe masarautun da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya kirkira a lokacin mulkinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da rushe masarautun da tsohon gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro.

Majalisar ta dauki wannan matakin ne a yau Alhamis 23 ga watan Mayu yayin zaman majalisar a Kano.

Sarakunan da abun ya shafa sune wanda Ganduje ya kirkira lokacin da yake kan madafun iko a jihar, cewar Freedom Radio.

Tun farko an sanya yau Alhamis 23 ga watan Mayu cewa majalisar dokokin Kano za ta yi duba tare da yanke hukunci kan kudirin gyaran dokar masarautun jihar.

Karin bayani na tafe ...

Asali: Legit.ng

People are also reading