Home Back

Mene ne bijirewar jiki ga sinadarin Insulin?

bbc.com 2024/5/10
Kayan marmari da abin gwajin jini

Asalin hoton, Getty Images

  • Marubuci, Somaya Nasr
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic

A shekaru biyu da suka gabata ana yawan magana a kan yadda jiki ke bijere wa sinadarin Insulin, a kafafen yada labarai da na sada zumunta. Baya ga wallafa litattafai da bidiyo da aka rinka yi.

Ana ta jan hankalin mutane a kan illar jiki ya bijire wa sinadarin Insulin wanda ya kan janyo babbar matsala ga lafiyar dan adam ciki har da cutar ciwon siga nau'i na biyu wato type 2 diabetes.

To ko ya jiki ke bijire wa sinadarin insulin da kuma alamomin da za a gane? Shin ko ana iya warkewa? shin ko azumi na taimaka wa wajen hana jiki ya bijire wa sinadarin insulin?

Asalin hoton, Getty Images

Kwayoyin halittar jini
Bayanan hoto, Sinadarin Insulin shi ke taimakawa wajen daidaita matsayin glucose a jikin dan adam

Mene ne sinadarin Insulin?

Wanda yake ajiye a cikin saifa, sinadarin insulin wani muhimmin abu ne a jikin ɗan'adam.

Aikinsa kuma shi ne daidaita sukari a cikin jini ta hanyar bai wa jiki damar ajiyewa da amfani da shi a matsayin makamashi.

Matsalolin lafiya da dama na iya faruwa idan saifa ba ta samar da wadataccen sinadarin insulin ko kuma gangar jiki ba ta iya amfani da shi yadda ya kamata.

Asalin hoton, Getty Images

Cikin jikin dan adam
Bayanan hoto, Cikin jikin dan adam

Yadda sinadarin insulin ke aiki a jikin dan adam

  • Jiki na mayar da abincin da mutum ya ci zuwa sukari, wanda ake gani shi ne babban abin da ke samar da kuzari a jikin dan adam
  • Sukarin na shi ga cikin jini sai ya sanar da saifa cewa to ga sukari nan don haka ta saki sinadarin insulin.
  • Sinadarin insulin na taimaka wa sukari a cikin jini ya shiga cikin tsoka da sauran wasu bangarori na jikin dan adam.
  • Idan sukari wato glucose ya shiga cikin kwayoyin halittar jiki yana rage jini kuma wannan alama ce cewa saifa ta daina samar da sinadarin insulin.

Asalin hoton, GETTY IMAGES / JUAN GAERTNER / SCIENCE PHOTO LIBRARY

Kwayoyin halitta
Bayanan hoto, Kwayoyin halitta

Me ake nufi da jiki ya bijire wa sinadarin Insulin?

Jiki ya bijirewa sinadarin insulin wani tsari ne mai sarkakiya da ke faruwa idan kwayoyin halitta a cikin tsoka da maiko da kuma hanta ba sa aiki kamar yadda ya kamata ta wajen sarrafa sinadarin insulin.

Hakan kuma na janyo wa wadannan abubuwa su daina ajiyewa ko rike sukari da ga cikin jini.

Daga nan sai saifa ta rinka yawan samar da sinadarin insulin wanda zai fi yawan sukarin a cikin jini abin da ke janyo wata cuta da ake cewa hyperinsulinemia.

To idan kuma kwayoyin halitta suka bijire wa sinadarin insulin, hakan na janyo yawan sukari a jikin mutum ya karu wanda a hankali hakan kan haifar da cutar ciwon suga nau'i na biyu.

Franklin Joseph, kwararre ne a bangaren kiwon lafiya a Birtaniya sannan kuma yana da kwarewa a bangaren cutar ciwon suga ya ce" Jiki ya bijire wa sinadarin insulin abu ne mai sarkakiya wanda kuma a wasu lokuta ana gado ko kuma yanayin tsarin rayuwar mutum ko muhallin da mutum yake duk na janyowa."

Asalin hoton, Franklin Joseph

Franklin Joseph
Bayanan hoto, Farfesa Franklin Joseph

Dalilan da ke sa jiki bijirewa Insulin

Farfesan ya ce akwai wasu dalilai da ke janyo haka:

  • Matsananciyar kiba: Yawan kitse musamman a ciki abin da ake gani kitse mai yawa, ana danganta shi a matsayin daya daga cikin abin da ke janyo jiki ya bijire wa sinadarin insulin.
  • Rashin motsa jiki: Matsalar rashin motsa jiki ko yin wasu aikace-aikace na taimakawa wajen sanya jiki ya bijire wa sinadarin insulin.
  • Gado: Wasu na gadar irin wannan yanayi na jiki ya bijirewa sinadarin insulin.
  • Rashin abinci mai gina jiki: Rashin cin abinci mai gina jiki na taimakawa wajen sanya jiki ya bijire wa sinadarin insulin.
  • Gajiya mai yawa:
  • Rashin bacci
  • Wata lalura: Idan mutum na da wata cuta kamar ciwon hanta ko wata matsala a mahaifa duk suna taimakawa wajen sanya jiki ya bijirewa sinadarin insulin.
  • Tsufa

Asalin hoton, Getty Images

Hoton wata da kuma faduwar rana
Bayanan hoto, Musulmi na azumi a lokacin watan Ramadan

Rawar da azumi ke takawa

Al'ummar Musulmi na azumi daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana a lokacin watan Ramadan.

Wata gidauniyar da ke kula da masu ciwon siga a Birtaniya ta nuna damuwa a kan masu fama da cutar musamman tsofaffi da wadanda jikinsu ya yi rauni.

"Yana da muhimmanci a tabbatar da mutanen da ke fama da cutar ciwon suga sun rinka yin azumi idan sun tabbatar sun tattauna da masu kula da irin ciwonsu." in ji farfesa Wasim Hanif, kwararre a bangaren masu lalurar ciwon siga a asibitin koyarwa na jami'ar Birmingham.

Shi kuwa Farfesa Joseph, cewa ya yi wasu binciken sun nuna cewa yin azumi na taimakawa ingancin sinadarin insulin, musamman ga mutanen da ke fama da lalurar bijirewar insulin din a jikinsu ko kuma masu fama da cutar ciwon siga nau'i na biyu.

To sai dai wasu na da tunanin cewa kasancewar wasu mutanen na fuskantar rama ko kuma wasu sauye-sauye a jikinsu a lokacin azumi, ya sa wasu ka iya samun illa a kan sinadarin insulin.

Farfesan ya ce, tasirin azumin watan Ramadan a kan masu fama da lalurar bijirewar jiki ga sinadarin insulin ya fi karfi ga tsofaffi ko masu fama da wata lalura.

Wata

Asalin hoton, Getty Images / Nur Photo

Wata masaniya a kan abinci, Reem Al-Abdallat, ta ce ya kamata mutane su rinka cin abinci mai gina jiki ko a lokacin azumi ko ma ba a lokacin azumin ba

Asalin hoton, Reem Al-Abdallat

 Reem Al-Abdallat
Bayanan hoto, Masaniyar abinci Reem Al-Abdallat

Azumi akai-akai

Yin azumi akai-akai ya janyo gagaruwamr muhawara inda wasu likitoci da masanan abinci ke magana a kan amfaninsa ga fannin lafiya.

Hakan dai ya hada da barin cin abinci zuwa wani lokaci a rana guda, da kuma cin abinci a kankanin lokaci.

Dr Nitin Kapoor, farfesa ne bangare da ya shafi ciwon siga da matsananciyar kiba a asibitin koyarwa na jami'ar Vellore da ke jihar Tamil Nadu a kudancin India.

Ya ce wasu makalu da aka gabatar sun nuna cewa yin azumi akai-akai na da nasa amfanin.To amma abin damuwar shi ne ba ga kowa ba.

Farfesa Joseph, ya ce kodayake binciken da aka yi a kan irin wannan azumi wato azumi akai-akai har yanzu ana samun ci gaba inda wasu ke ganin zai taimaka wajen inganta matsayin sinadarin insulin a jikin dan adam.

Asalin hoton, Getty Images / RichLegg

Wata mata na gwada matsayin sinadarin insulin dinta
Bayanan hoto, Wata mata na gwada matsayin sinadarin insulin dinta

Alamomin yadda jiki ke bijirewa sinadarin insulin

Alamomin farko ko gargadin farko na bijirewar jiki ga sinadarin insulin ba lallai a gane su ba.

To amma akwai wasu alamu da ke nuna cewa jikin dan adam ya fara bijirewa sinadarin insulin.

A cewar farfesa Joseph, alamomin sun hada da karuwar jin yunwa da gajiya da rama da fatar mutum ta rinka baki musamman ta wajen wuyansa da hammata, da hawan jini da yawan maiko a jikin mutum da dai sauransu.

Ya kara da cewa idan mutum ya kamu da cutar ciwon siga saboda bijirewar jiki ga sinadarin insulin to daga nan zai ci gaba da fuskantar wasu alamomi.

Ya ce idan ka fara jin wadannan alamomi sai ka yi maza ka je wajen likita ko kwararru don a gano ainihin matsalar.

Asalin hoton, Getty Images

Wata mata na gwada jininta
Bayanan hoto, Bijirewar jiki ga sinadarin insulin na janyo cutar siga

Yaya nike abinci da aikewa da sikari zuwa jini yake?

Ana amfani da tsarin nike abinci da aikewa da sikari zuwa jini ne domin a bambanta irin abincin da ake ciki da kuma tasirinsu da sikari a cikin jini.

Ana kuma duba ko abincin da mutum ke ciki zai iya rage ko kara yawan sikarin da ke cikin jikin mutum

Abincin da ke sa kuzari da aka fi sani da Carbohydrates, ana ganin su kamar suna da karancin tsarin nike abinci da aikewa da sikari zuwa jini.

Tufa da abin gwajin jini da kuma magunguna

Asalin hoton, Getty Images / MartinFredy

Asalin hoton, Getty Images

Sikari mai 'ya'ya
Bayanan hoto, Sauyi a rayuwa da kuma magunguna na taimakawa wajen dakile matsalar bijirewar jikin ga sinadarin insulin

Masaniyar abinci Reem Al-Abdallat, ta shawarci masu matsalar bijirewar jiki ga sinadarin insulin da su mayar da hankali a kan sanin abincin da suke ci, dole su rage shan zaki da kuma cin abinci masu sitati.

Shawara ta biyu kuma a cewarta ita ce su rinka motsa jiki akai-akai.

Asalin hoton, Getty Images

Nau'ikan abinci masu gina jiki
Bayanan hoto, Nau'ikan abinci masu gina jiki

Gajiya mai yawa ta na janyo wannan matsala, don haka ya kamata masu irin wannan matsala su samu hanyar da za su rage ta kamar ta yin atisayen yoga da sauran abubuwa na motsa jiki.

Sannan samun isasshen bacci ma na taimakawa in ji Farfesa Joseph.

Asalin hoton, Getty Images

Mutane na motsa jiki
Bayanan hoto, Mutane na motsa jiki

Daga karshe magunguna irinsu Metformin na taimakawa wajen rage bijirewar jiki ga sinadarin insulin.

Sannan neman shawarwari a wajen kwararru duk na taimakawa.

People are also reading