Home Back

Ministan Harkokin Waje Ya Kai Karar Babban Sakatare Kan Zargin Alfasha

leadership.ng 2024/6/26
Ministan Harkokin Waje Ya Kai Karar Babban Sakatare Kan Zargin Alfasha

Da alama Babban Sakatare Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar, Ambasada Adamu Lamuwa na cikin halin ha’ula’i sakamakon zargin neman tarawa da wata ma’aikaciya da ake yi masa.

Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ya rubuta wasika zu-wa ga ofishin Shugabar Ma’aikatan tarayya, Dr. Folasade Yemi-Esan, inda ya bukaci ta dauki mataki kan Lamuwa bisa zargin cin zarafin Misis Simisola Fajemi-rokun.

Takardar korafin na kunshe ne a cikin wata wasika da aka mika wa manema laba-rai, mai kwanan wata 27 ga Mayu, 2024, mai take; ‘RE: Korafi a Hhukumance Game da cin zarafin Misis Simisola Fajemirokun Ajayi wanda Ambasada Ibrahim Adamu Lamuwa (Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Waje ya yi)”

A cikin wasikar da ya sanya wa hannu, ministan ya ce, “Ya zama dole in rubuta domin in sanar da ku karar da aka shigar a kan babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen kasar nan, Ambasada Ibrahim Adamu Lamuwa kan zargin cin zaraf-in mata.“Bisa la’akari da girman al’amarin, ina ganin ya zama dole in jawo hankalinku kan lamarin domin lura da shi yadda ya kamata.

“Muna rokkon a hada da kwafin takardar korafin da na samu ta sakon imel. Kuma a shirye nake da na baku duk wani goyon baya da hadin kai da kuke bukata game da lamarin domin ganin kun sauke duk nauyin da ya rataya a wuyanku.”

Da aka tuntubi mai bai wa minista Alkassim Abdulkadir shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabarun sadarwa, cewa ya yi, “Hukumomin da suka dace na bin diddigin lamarin.”

Kundin tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya na shekarar 1999 da aka yi yi wa kwaskwarima bai amince da cin zarafi ta fuskar jima’i ba.
Sashe na 352 ya bayyana cewa “Duk mutumin da ya ci zarafin wani da nufin ya ni’imtu da jikinsa ko jikinta bisa jin dadi na al’ada ya tafka babban laifin da zai bayu zuwa hukiuncin dauri na shekaru 14 a gidan kaso.

People are also reading