Home Back

Amurka Za Ta Aika Wa Ukraine Karin Makamai Masu Linzami

leadership.ng 2024/7/3
Amurka Za Ta Aika Wa Ukraine Karin Makamai Masu Linzami

Wasu jami’an Amurka biyu sun ce shugaba Joe Biden ne ya amince da matakin tura makaman.
Amurka za ta aika wa Ukraine makami mai linzami na Patriot, a cewar wasu jami’an Amurka biyu, a matsayin maida martani ga kiraye-kirayen da Kyib ta yi na neman taimakon gaggawa wajen samun karin na’urorin kariya ta sama yayin da kasar ke fama da hare-haren Rasha a yankin Kharkib.
Wannan zai zama makami mai linzami samfurin Patriot na biyu da Amurka ta bai wa Ukraine, ko da yake ma’aikatar tsaron Pentagon ta tura makamai masu linzami da ba a bayyana adadinsu ba.

Sauran kasashen kawancen Ukraine da suka hada da Jamus, su ma sun sama wa Ukraine da na’urorin kariya ta sama da kuma alburusai.

Jami’an na Amurka biyu sun yi magana ne bisa sharadin a sakaya sunayensu saboda ba a sanar da matakin ba. Jaridar New York Times ce ta fara ba da rahoton matakin.
A karshen watan da ya gabata, shugaban Ukraine Bolodymyr Zelenskyy ya nemi karin makami mai linzamin Patriot na Amurka, yana mai cewa makaman za su taimaka wa dakarunsa wajen kakkabo bama-bamai kusan 3,000 da Ra-sha ke harbawa cikin kasar duk wata.

Da yake magana a Madrid, Zelenskyy ya ce har yanzu Ukraine na bukatar karin wasu makaman guda bakwai don dakile hare-haren da Rasha ke kai wa kan manyan na’urorin samar da wutar lantarki da yankunan farar hula, da ku-ma wuraren soja.

Ya ce Ukraine na bukatar biyu daga cikin makaman don kare Kharkib, inda Rasha ta kaddamar da hare-haren tsallaken iyaka a ranar 10 ga watan Mayu, lamarin da ya sa har yanzu sojojin Ukraine ke gwagwarmaya.

“Idan muna da wadannan makaman na Patriot na zamani, jiragen sama na Ra-sha ba za su iya zuwa kusa su jefa bama-bamai a kan farar hula da sojoji ba,” in ji Zelenskyy a wani taron manema labarai a babban birnin Sipaniya.

People are also reading