Home Back

Amurka ba za ta juya wa Ukraine baya ba - Lioyd Austin

dw.com 2024/5/4
Babban sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin
Babban sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin

Amurka ta kara jaddada goyon bayanta ga Ukraine wannan kuwa duk da tangardar da aka samu na kin amincewa da wani kunshin tallafin kudin makamai daga majalisar dokokin kasar.

Da yake jawabi a yayin bude taron kasashe kawayen Ukraine a sansanin Ramstein a Jamus, babban sakataren harkokin tsaron Amurka Lioyd Austin, ya ce Amurka ba za ta juya wa Ukraine baya ba komai rintsi.

Lioyd Austin ya kara da cewa mun sha alwashin ba wa Ukraine dukkanin tallafin da take bukata domin ta jajirce daga mamayar da take fuskanta daga Rasha.

People are also reading