Home Back

Jam'iyyar hamayya ta yi gagarumar nasara a zaɓen Turkiyya

bbc.com 2024/5/4
Magoya bayan 'yan hamayya a Turkiyya na murna

Asalin hoton, REUTERS/Umit Bektas

Jam’iyyar Shugaba Erdogan, A-K, ta yi rashin nasarar da ba ta taba yi ba a zabukan manyan biranin kasar ta Turkiyya.

Babbar jam’iyyar hamayya ta C-H-P, ta samu nasararta mafi girma a cikin kusan shekara 50, yayin da aka kirga kusan dukkanin kuri’un da aka kada a zaben da aka yi jiya Lahadi.

Sakamako ya kasance sabanin abin da Shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya yi fata na sake kama iko da manyan biranen kasar, a kasa da shekara daya da nasarar da ya samu ta zarcewa a matsayin shugaban kasar a wa’adinsa na uku kuma na karshe bisa tsarin mulki.

Shugaban ya jagoranci yakin neman zabe ga dan takarar jamiyyarsa, ta AP Murat Kurum, tsohon ministan muhalli da birane mai shekara 47, a birni mafi yawan jama’a, har miliyan 16, Santanbul, a miliyan kusan 85, na yawan 'yan kasar.

Birnin ya kasance mahaifar shugaban, kuma inda ya kasance matakinsa na shiga siyasa da ya zama magajin gari har kuma likkafarsa ta daga ya zama shugaban kasar.

Dan takarar jam’iyyar hamayya ta C-H-P, wadda ba ruwanta da sha’anin addini, wanda kuma shi ne ke rike da kujerar magajin garin, Ekrem Imamoglu, wanda nasararsa a wancan zaben shekara biyar baya, ta daburta lissafin kaka-gidan da Mista Erdogan ya dade yana yi, shi ne ya kara nasara, inda ya wuce abokin karawar tasa da sama da kashi goma cikin dari.

Kuma ana daukar Mista Imamoglun a matsayin wanda zai iya kasancewa mai kalubalantar Erdogan, da jamiyyarsa a zaben shugaban kasar a shekara hudu mai zuwa

Wani mazaunin birnin na Santanbul ya bayyana dalilinsu na zaben Mista Imamoglun:

Ya ce, ‘’ Shi ne muryar, wadanda aka danne, wadanda dokokin karfa-karfa suka muzgunawa, talakawa, tsofaffi, wadanda ko sakon tuwita ba za su iya turawa ba, wadanda ba a iya jin muryarsu. Muna son mu yi magana a ji mu yanzu. Muna son mu kalubalnaci Imamoglu, mu yi masa tsawa shi ma. Muna son ganin kasar da za mu iya kumaji ba tare da takura ko wani tashin hankali ba.’’

Jam’iyyar hamayyar ta yi nasara a dukkanin manyan biranen kasar biyar da suka hada da Santanbul, mai yawan jama’a miliyan 16.

Shugaba Erdogan ya amince da rashin nasarar da jamiyyar tasa ta yi amma ya ce hakan bai kawo karshensu ba, kuma za su je su yi karatun ta-natsu, su kori ba.

People are also reading