Home Back

Ana Tsaka da Ricikin Siyasa: Gwamnan PDP Ya Rantsar da Sababbin Ciyamomi 23 a Jiharsa

legit.ng 2024/7/5
  • Gwamna Siminialayi Fubara na Ribas, ya rantsar da sababbin shugabannin kwamitocin riko na kananan hukumomi 23 na jihar
  • An gudanar da bikin rantsuwar ne a gidan gwamnatin jihar dake Fatakwal, babban birnin jihar a safiyar Laraba
  • Wannan na zuwa ne bayan da gwamnan ya aike da sunayen shugabannin rikon zuwa majalisar jihar domin tantance su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Fatakwal, Jihar Ribas - Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya rantsar da sababbin shugabannin riko na kananan hukumomi 23 na jihar.

An yi bikin rantsuwar ne a ranar Laraba a gidan gwamnati da ke Fatakwal, babban birnin jihar cikin tsauraran matakan tsaro.

Fubara ya rantsar da sababbin shugabannin riko na jihar Ribas
Ribas: Fubara ya rantsar da ciyamomi 23 na jiharsa. Hoto: @SimFubaraKSC Asali: Facebook

Majalisar Ribas ta tantance ciyamomi 23

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa an gudanar da bikin ne a zauren majalisar zartarwar jihar inda kashin farko na shugabannin rikon su 11 suka karbi rantsuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan Fubara ya mika jerin sunayen ga majalisar dokokin jihar karkashin jagorancin kakakin majalisar, Victor Jumbo.

‘Yan majalisar dai sun gayyaci wadanda aka mika sunayensu domin tantance su da misalin karfe 8 na safiyar Laraba, in ji rahoton Vanguard.

Jerin sunayen ciyamomin da aka rantsar

Duba sunayen shugabannin riko 23 da Fubara ya rantsar da su a kasa:

Sunan ciyaman Karamar hukuma
1 Madigai Dickson Abua/Odua
2 Happy Benneth Ahoada ta Gabas
3 Mr. Daddy John Green Ahoada ta Yamma
4 Otonye Briggs Akuku Toru
5 Reginald Ekaan Andoni
6 Orolosoma Amachree Asari Toru
7 Alabota Anengi Barasua Bonny
8 Anthony Soberekon Degema
9 Brain Gokpa Eleme
10 David Omereji Emouha
11 John Otamiri Etche
12 Kenneth Kpeden Gokana
13 Darlington Orji Ikwerre
14 Marvin Yobana Khana
15 Chijioke Ihunwo Obia/Akpor
16 Princewill Ejekwe Ogba/Egbema/Ndoni
17 Evans Bipi Ogu/Bolo
18 Princess Ogan Okrika
19 Promise Reginald Omuma
20 Enyiada Cookey-Gam Opobo/Nkoro
21 Gogo Philip Oyigbo
22 Ichemati Ezebunwo Port Harcourt
23 Matthew Dike Tai

Obasanjo ya maganku kan nasarar gwamnatinsa

A wani labarin, mun ruwaito Olusegun Obasanjo ya bugi kirji da cewa gwamnatinsa na daga cikin mafi nagarta wajen gudanar da mulki a tarihin Najeriya.

Olusegun Obasanjo ya ce gwamnatinsa na daga cikin mafi nagarta wajen gudanar da mulki a tarihi, wadda ta taimakawa dimokuraɗiyyar kasar na shekaru 25.

Asali: Legit.ng

People are also reading