Home Back

Shugaban CIA ta Amurka zai je Masar kan batun yakin Gaza

dw.com 2024/10/6
Hoto: MANDEL NGAN/AFP/Getty Images

Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Amurka William Burns na shirin kai ziyara Masar, don tattauna hanyoyin tsagaita wuta a yakin Gaza, kamar yadda gidan talabijin din Masar na Al Qahera ya rawaito a Lahadin nan.

Haka zalika Mr Burns zai kai ziyara Qatar, kafin daga bisani ya gana da tawagar gwamnatin Isra'ila, domin lalubo bakin zaren tsayar da yakin baki daya.

Yakin dai ya barke ne tun bayan harin ba-zata da kungiyar Hamas mai gwagwarmaya da makamai a yankin Zirin Gaza na Falasdinu ta kai Isra'ila a ranar bakwai ga watan Oktoban bara, kuma kawo yanzu yakin ya yi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa sama da dubu talatin da takwas.

People are also reading