Home Back

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 5, Sun Saki 51 Bayan Biyan Fansa A Kaduna

leadership.ng 2024/5/12
'Yan Bindiga

Wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da mutane 61 a kauyen Budah Hausa da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna makonni uku da suka gabata sun kashe biyar daga cikin wadanda suka sace.

Mutum 51 da aka sako, an rahoto cewa, sun shaki iskar ‘yanci ne a ranar Talata bayan biyan kudin fansa, da kuma tarin kwayoyi da babura da barayin suka nema.

‘Yan Bindigar sun kuma ci gaba da tsare Biyar daga cikin wadanda suka sacen, acewarsu, kudin fansar ya yi kadan, sai an karo kafin su sako su.

Wani jami’in ‘yan banga a yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar wa manema labarai sakin nasu a ranar Alhamis, inda ya ce, dukkan mutanen biyar din da aka kashe maza ne.

People are also reading