Home Back

Rashin Tsaro: Gwamnatin Zamfara Ta Dauki Matakin Kawo Karshen Matsalar

legit.ng 2024/5/15
  • Gwamnatin jihar Zamfara ta ɗauki matakin taƙaita zirga-zirga a iyakokinta da jihohin Katsina da Sokoto
  • Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta ɗauki wannan matakin ne domin daƙile ayyukan ƴan bindiga
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar wanda ya sanar da ɗaukar matakin ya ce dokar za ta yi aiki ne daga ƙarfe 7:00 na yamma zuwa ƙarfe 6:00 na safe

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta bada umurnin taƙaita zirga-zirga cikin gaggawa a kan iyakokin jihar da jihohin Katsina da Sokoto daga ƙarfe 7:00 na yamma zuwa ƙarfe 6:00 na safe.

Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na jihar, Alhaji Mannir Haidara ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Gusau, a ranar Talata, 2 ga watan Afrilun 2024, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Gwamnatin Zamfara ta sa dokar takaita zirga-zirga
Gwamnatin Zamfara ta sa dokar takaita zirga-zirga a iyakokinta da Katsina/Sokoto Hoto: @Mfareeees Asali: Twitter

Haidara ya bayyana cewa wannan umurnin na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka domin daƙile ayyukan ta'addanci a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa wannan sabon umurnin zai fara aiki ne nan take ba tare da ɓata wani lokaci ba, rahoton jaridar Daily Post ya tabbatar.

Meyasa gwamnatin Zamfara ta sanya dokar?

A kalamansa:

"Tun daga yau gwamnatin jiha ta bayar da umarnin taƙaita zirga-zirga a kan iyakokin Katsina/Zamfara da Sokoto/Zamfara.
"Wannan ya haɗa da Yankara a ƙaramar hukumar Faskari, jihar Katsina kan iyakar Zamfara da Katsina da kuma iyakar Bimasa Zamfara da Sokoto daga ƙarfe 7:00 na yamma zuwa ƙarfe 6:00 na safe a kullum.
"An yi haka ne domin a magance matsalar sace-sacen matafiya da ake yi a kan titin babbar hanyar Sokoto-Gusau-Funtua.
"Wannan wani ɓangare ne na matakan da gwamnatin jiha ta ɗauka na ragewa tare da magance ayyukan sace-sacen mutane da ƴan bindiga ke yi, musamman a manyan titunan jihar.

Kwamishinan ya shawarci masu ababen hawa da matafiya da su bi wannan umurni, domin a cewarsa an ɗauki matakin ne domin kare lafiyarsu.

Zamfara ta zama matattarar ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya koka kan yadda jihar ta zama matattarar ƴan bindiga.

Gwamnan ya bayyana cewa idan ana son a kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya, dole sai an magance matsalar a jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

People are also reading