Home Back

Nijar ta sanar da dakatar da tura man fetur dinta zuwa Benin

dw.com 2024/7/2
Hoto: Yanick Folly/AFP/Getty Images, ORTN/TÈlÈ Sahel/AFP

Jamhuriyar Nijar ta sanar da dakatar da tura danyen man fetur dinta zuwa Jamhuriyar Benin, har sai Benin din ta saki jami'anta na kamfanin WAPCO da ta tsare tun ranar Laraba.

Ministan man fetur din kasar Mahaman Moustapha Barke ya sanar da hakan, a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da ministan shari'a na kasar da ya kira a Alhamis din nan a birnin Yamai.

...CLIP Minista Barke...

Ya ce''idan har zuwa karfe biyar na yammacin yau ba a saki jami'an ba aka kuma ba su izin komawa aikinsu na sa ido ga lodin man cikin jirgin ruwa, za mu dakatar da aikin babbar cibiyar man ta Kulele, ta yadda ba za a samu damar iya yin lodin man a cikin jirgin ruwan da ke girke ba, kuma ba za mu sake aika ko da digon man a cikin bututun ba, har sai lokacin da Benin ta amince da kiyaye alkawurran da ta dauka''.

Nijar din ta yi barazanar kai karar Jamhuriyar Benin gaban kotun kasa da kasa, kan rashin mutunta yarjejeniyar aikin man da ta hada kasashen biyu da ma Chaina.

Haka zalika hukumomin Nijar sun zargi Chaina da nuna ha'inci a cikin lamarin, bayan da suka amince su loda man na Nijar ba tare da kasancewar wakilan Nijar ba.

People are also reading