Home Back

Ana Kukan Abinci Ya Yi Tsada, ’Yan Najeriya Na Shan Lita Biliyan 1.6 Ta Madara a Shekara

legit.ng 2024/7/7
  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa 'yan Najeriya na shan lita biliyan 1.6 ta madara yayin da take kashe dala biliyan 1.5 a kowacce shekara
  • Karamin ministan noma da samar da abinci, Sanata Aliyu Abdullahi ya bayyana hakan a taron bikin ranar madara ta duniya ta 2024
  • Sanata Abdullahi ya ce taken bikin a Najeriya shi ne: “Samar da madara mai gina jiki da kuma nemo masu zuba jari a harkar sarrafa madara."

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Karamin ministan noma da samar da abinci, Sanata Aliyu Abdullahi, ya ce ‘yan Najeriya na shan kimanin lita biliyan 1.6 na madara a duk shekara.

Sanata Abdullahi ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Asabar a Abuja domin bikin ranar madara ta duniya ta 2024.

Gwamnati ta yi magana kan samar da madara a Najeriya
Gwamnati ta bayyana adadin madarar da 'yan Najeriya ke sha a shekara. Hoto: @NGfmafs/X, Skynesher/Getty Images Asali: Getty Images

Karamin ministan ya ce kashi 60 na kayayyakin madara ana shigo da su ne daga kasashen waje, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2024: Bikin ranar madara ta duniya

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa, 1 ga watan Yuni, ita ce ranar da aka kebe domin bikin ranar madara ta duniya.

Taken bikin ranar madara ta duniya a bana shi ne: "Mu yi bikin murnar sarrafa madara mai gina jiki da dorewa."

Sanata Abdullahi ya ce taken bikin a Najeriya shi ne: “Samar da madara mai gina jiki da kuma nemo masu zuba jari a harkar sarrafa madara."

2024: An sha lita 1.6b ta madara a Najeriya

Jaridar PM News ta ruwaito ministan na cewa Najeriya na kashe dala biliyan 1.5 a duk shekara wajen shigo da kaso 60 na madara da kayayyakin ta.

“Wannan ya faru ne saboda gibin da ake samu wajen samar da madara a kasar, yayin da ‘yan Najeriya ke shanye akalla lita biliyan 1.6 na madara da kayayyakin ta a shekara.
"Burin shugaban kasa Bola Tinubu shi ne mu samu wadataccen abinci a kasa ta yadda za mu rika fitar da kayayyakin madara zuwa kasashen Afirka a karkashin yarjejeniyar AfCFTA)."

- In ji Sanata Abdullahi.

Sarrafa rogo zuwa sinadarin fetur a Enugu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya da ta jihar Enugu sun kulla yarjejeniyar noman rogo da sarrafa shi zuwa sinadarin fetur.

Wannan yarjejeniyar wadda aka yi nasara a matakin gwaji, za ta taimaka wajen habaka noman rogo da bunkasa tattalin arziki, tare da magance rashin aikin yi da rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

People are also reading