Home Back

Matsayin Slovakia na tasiri a zaben 'Yan Majalisar EU

dw.com 2024/7/7
Wasu mata masu kada kuri'a a zaben EU a birnin Bratislava na Slovakia
Wasu mata masu kada kuri'a a zaben EU a birnin Bratislava na Slovakia

A kasar Slovakia zaben ya zo ta tarnaki na yunkurin halaka Firaiministan kasar Robert Fico, a ranar 15 ga watan Mayun 2024, wanda hakan zai yi tasiri a kuri'un al'ummar kasar kimanin milyan 5.4. Masu sharhi kan zaben sun ce harin da aka kai wa Firaimistan zai bawa jam'iyyar Firimiyan kasar nasara.Shugabannin EU sun amince da sabuwar taswira

Karin bayani: Zaben majalisar dokokin Turai na 2024 

Fico, wanda ke gaba-gaba a goyon bayan Rasha da kuma sukar manufofin Amurka, ya ki yin tsokaci kan zaben duk da cewa a baya bayannan  ya ce yana fama da adawa daga mambobin kasashen EU kasancewar ra'ayinsu bai zo daya ba.

People are also reading