Matsayin Slovakia na tasiri a zaben 'Yan Majalisar EU
A kasar Slovakia zaben ya zo ta tarnaki na yunkurin halaka Firaiministan kasar Robert Fico, a ranar 15 ga watan Mayun 2024, wanda hakan zai yi tasiri a kuri'un al'ummar kasar kimanin milyan 5.4. Masu sharhi kan zaben sun ce harin da aka kai wa Firaimistan zai bawa jam'iyyar Firimiyan kasar nasara.Shugabannin EU sun amince da sabuwar taswira
Karin bayani: Zaben majalisar dokokin Turai na 2024
Fico, wanda ke gaba-gaba a goyon bayan Rasha da kuma sukar manufofin Amurka, ya ki yin tsokaci kan zaben duk da cewa a baya bayannan ya ce yana fama da adawa daga mambobin kasashen EU kasancewar ra'ayinsu bai zo daya ba.