Home Back

Wadatar Abinci: Za Mu Kara Zuba Jari A Aikin Noman Bana –Gwamna Buni

leadership.ng 2024/6/2
Takarar Tinubu Da Shettima Babbar Nasarar APC Ce – Buni

Gwaman Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayyana cewa; gwamnatinsa za Ta kaddamar da babban shirin aikin noma, wanda zai taimaka wa farfado da aikin noman na bana a fadin jihar, don kara samar da wadatacen abinci da kuma magance kalubalen rashin tsaro a jihar.

Buni ya kara da cewa, manufar shirin shi ne; don kara samar da ayyukan yi, musamman a tsakanin matasan jihar domin inganta rayuwarsu ta gobe.

Gwamnan ya bayyana hakan ne, a cikin wata sanarwa da hadiminsa na yada labarai, Mamman Mohammed ya bayar.

Kazalika, ya bukaci matasan jihar da su yi kokarin amfani da wannan dama, don kara fadada aikin noma a yankunan nasu.

Acewar tasa, gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen bunkasa aikin noma, musamman ganin yadda manoman jihar za su amfana da samun dimbin kudaden shiga.

People are also reading