2027: Gwamna Ya Yi Magana Kan Rade Radin Daukarsa Mataimakin Atiku a Zabe
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bayelsa - Gwamna Douye Diri ya yi martani kan jita-jitar daukarsa mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2027.
Diri ya yi fatali da bukatar da wata kungiya ta yi domin Atiku ya dauke shi a matsayin mataimakinsa a zaben shugaban kasa.
Leadership ta tattaro wata kungiya ce mai suna Diri Angles ta ba da shawarar daukar gwamnan a zaben 2027 da ke tafe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai gwamnan ya barranta kansa da wannan kira inda ya bukaci al'umma da su yi watsi da shawarar domin ba ya bukata.
Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin sakataren yada labaransa, Daniel Alabrah a jiya Laraba 3 ga watan Yulin 2024, kamar yadda Punch ta ruwaito.
"Ban rudu da wannan kira da ake yi ba, a siyasa ta na dogara da ubangiji ne ba wai wasu 'yan siyasa da kulle-kullesu ba."
"Bukatar wadanda suka yi hakan shi ne kawo matsala sai dai ba su yi nasara ba saboda ba ni bukatar hakan ko kadan."
- Douye Diri
A wani labarin, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ziyarci Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura.
An yi ta rade-radin cewa Atiku ya kai ziyarar domin shirye-shiryen zaben 2027 da ake tunkara domin kwace mulkin Bola Tinubu
Sai dai a bangarensa, Atiku ya ce babu wani shirin siyasa a ziyarar kawai ya kai gaisuwa ne ga Buhari bayan kammala bukukuwan sallah.
Asali: Legit.ng