Home Back

“Ba Za Mu Iya Ba”: ALGON Ta Dauki Matsaya Kan Sabon Mafi Karancin Albashin N62,000

legit.ng 2024/10/5
  • Kananan hukumomin Najeriya ba za su iya biyan ma’aikata N62,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ba, in ji kungiyar ALGON
  • Kungiyar ALGON ta ce da yawan kananan hukumomi ba sa iya biyan N30,000 da aka amince da shi a 2019 balle a yi maganar N62,000
  • Shugaban ALGON na kasa, Aminu Muazu-Maifata ya nemi a tsayar da mafi karancin albashi da zai iya dorewa ba marar yiwuwa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar kananan kukumomin Najeriya (ALGON) ta ce zai yi wahala kananan hukumomi su iya biyan ma’aikata N62,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi.

A ranar 7 ga watan Yuni ne gwamnatin tarayya ta kara tayin sabon mafi karancin albashin ma’aikata daga N60,000 zuwa N62,000 amma kungiyar kwadago ta dage kan N250,000.

ALGON ta yi magana kan sabon mafi karancin albashi
ALGON ta yi matsaya kan biyan N62,000 a matsayin sabon albashi. Hoto: Aminu Muazu Maifata Asali: Facebook

Da yake tattaunawa da gidan talabijin na Channels, a ranar Alhamis, shugaban ALGON na kasa, Aminu Muazu-Maifata, biyan N62,000 abu ne mai wahala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muazu-Maifata ya ce har yanzu wasu daga cikin kananan hukumomi 774 na kasar nan na fafutukar biyan mafi karancin albashin N30,000 da aka amince da shi a 2019.

"Ba za mu iya biyan N62,000 ba" - ALGON

Shugaban ALGON ya ce:

"Bisa la'akari da kason da ake samu daga asusun FAAC, babu wata karamar hukuma a Najeriya da za ta iya biyan N62,000, balle ayi maganar biyan N250,000."
“Kananan hukumomi 774 na samun abin da bai haura kaso 18 na jimillar kudaden da FAAC ke rabawa ba, yayin da gwamnatin tarayya ke samun sama da kashi 52.
“Wasu kananan hukumomin ma ba sa iya biyan N30,000, akwai inda har yanzu suna biyan N18,000. Duk abin da FAAC ke bayar wa na tafiya ne ga albashi da fansho."

Shugaban kungiyar ta ALGON ya nemi kungiyoyin kwadago da ma gwamnatin tarayya da ta sanya mafi karancin albashi da zai iya dorewa ba wai abin da ba zai yiwu ba.

Kalli bidiyon tattaunawar a nan kasa:

Kungiyar kwadago ta aika bukata ga Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa hadaddiyar kungiyar kwadago ta gargadi Shugaba Bola Tinubu da ya kada ya kuskura ya aika wa majalisar tarayya sabon mafi karancin albashi ba tare da ya tuntube ta ba.

A cewar kungiyoyin, tuntubar wadanda ya dace kan sabon mafi karancin albashi zai haifar da daidaiton ma'aikata da gwamnati a kasar.

Asali: Legit.ng

People are also reading