Home Back

Hukumomin Saudiyya sun Gargadi Maniyyata a Shirin Hajjin Bana

legit.ng 2024/7/3
  • Hukumomi a kasa mai tsarki sun yi gargadin cewa za a fuskanci tsananin zafi a aikin hajjin bana yayin da musulmi ke shirin fara sauke farali
  • A ranar 14 Yuni, 2024 ne musulmin duniya za su fara aikin hajjin bana, sai dai cibiyar kula da yanayi ta kasar Saudiyya na cewa zafin zai kai digiri 44
  • Shugaban cibiyar kula da yanayi ta Saudiyya, Ayman Ghulam ya shaidawa musulmi za a samu karuwar zafi fiye a kima a Makkah da Madina

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Saudi Arabia- Hukumomin kasa mai tsarki sun gargadi maniyyatan aikin hajjin bana da cewa za a fuskanci tsananin zafi a aikin hajjin bana da za a fara ranar 14 Yuni, 2024.

Shugaban cibiyar kula da yanayi ta kasar Saudiyya, Ayman Ghulam ya shaidawa manema labarai cewa akalla, za a fuskanci tsananin zafi a kan ma’aunin Celsius 44.

Aikin hajji
Za a yi tsananin zafi a bana- hukumomin Saudiyya Hoto: National Hajj Commission of Nigeria Asali: Facebook

RFI ta ruwaito cewa hasashe ya nuna cewa zai yi wahala a samu ruwan sama, sannan za a samu karuwar zafin rana a biranen Makkah da Madina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zafi ya kawo cikas a hajjin 2023

Yayin aikin hajjin bara, akalla musulmin duniya miliyan 1.8 ne suka sauke farali a kasa mai tsarki, kuma an samu da yawa daga cikinsu sun fuskanci matsalolin zafi.

Alkaluman da hukumar kula da yanayi ta kasar Saudiyya ta fitar ya bayana cewa akalla mutane 2,000 da cutukan da suka danganci zafi ya fitar, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.

Daga matsalolin da musulmi suka fuskanta saboda tsananin zafi a shekarar da ta wuce akwai shanyewar jiki, gajiya, kurajen zafi da dole ya sanya aka kwantar da wasu daga cikinsu.

Akalla mahajjata 240 ne daga kasar Indonesia suka rasu yayin aikin hajjin 2023, da wasu da yawa daga sauran kasashe da suka sauke farali.

Hukumomi za su kora maniyyatan daga Saudiyya

A baya mun ruwaito muku cewa hukumomi a kasa mai tsarki sun ce za su koro maniyyatan aikin hajjin bana da suka karya dokoki.

Sanarwar da jami'ar hulda da jama'a ta hukumar NAHCON, Fatima Usara ta fitar, ta yi gargadin za a koro mahajjatan tare da dora musu tara.

Asali: Legit.ng

People are also reading