Home Back

KOWA YA SAMU RANA YA YI SHANYA: Yadda Tinubu ya bayar da kwangiloli 13 cikin duhu, ya bar ‘yan Najeriya a cikin duhu

premiumtimesng.com 2024/9/27
Tinubu ya rattaba hannu kan sabon kudirin ba da lamuni na dalibai

Cikin makon shekaranjiya ne Fadar Shugaban Ƙasa ta watsa jerin kwangiloli da tsare-tsaren gwamnatin tarayya guda 20, waɗanda Majalisar Zartaswa ta amince da su, a taron ta na ranakun Talata da Litinin.

Sai dai kuma Shugaban Ƙasa Bola Tinubu bai bayyana wasu muhimman batutuwa da suka zama wajibi jama’a su sani ba, kamar sunayen ‘yan kwangilar da aka ba aiki, adadin kuɗaɗen kwangilar da wa’adin lokutan da kwangiloli za su kai kafin a kammala.

Kwangiloli 16 da ke cikin jerin ayyukan dai duk su na bisa tsarin Dokar Kwangiloli ‘Public Procurement Act’, amma kuma guda 3 ne kaɗai aka bayyana sunayen ‘yan kwangilar, adadin kuɗin kwangilar da kuma lokacin kammalawa.

Hakan ya nuna shakku cewa ana lulluɓe wasu bayanai, ko ana yin ƙumbiya-ƙumbiya a asirce. Domin sauran ayyukan kwangiloli 13 duk akwai alamar tambaya a kan su.

Wannan jarida ta tattauna da masana daban-daban a fannin bin-diddigin kwangiloli da ƙungiyoyin sa-ido da na kare haƙƙi, waɗanda duk suka nuna shakku a kan kwangilolin.

Ayo Ladipo ta BudgiT ta ce kwangilar ginin Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja akwai alamar tambaya a kan ta. An ware mata Naira biliyan 37. Amma fa ita ce a kasafin 2023 aka ware wa Naira biliyan 10 kacal. “To ta yaya kuma yanzu kuɗin ya koma Naira biliyan 37 daga Naira biliyan 10?”

Ga Jerin Wasu Kwangiloli Da Gwamnatin Bola Tinubu Ta Bayar A Cikin Duhu:

A makon jiya ne dai wannan jarida ta buga labarin cewa Gwamnatin Tinubu ta kinkimo ayyukan raya ƙasa guda 20, ciki har da sayo tulin motocin sauƙaƙa zirga-zirga.

Gwamnatin Tarayya ta bijiro da ayyukan raya ƙasa guda 20 a zaman da Majalisar Zartarwa ta yi ranar Talata, a Babban Ɗakin Taro na Fadar Shugaban Ƙasa.

Bayan an ɗauki dogon lokaci ana ganawa, a ƙarshe dai an zartas da amincewa kan wasu ayyukan raya ƙasa waɗanda za su bunƙasa tattalin arziki, su jawo masu zuba jari tare da sauƙaƙa hanyoyin gudanar da kasuwanci a cikin ƙasa.

Wannan jarida ta gano cewa daga cikin ayyuka 16, guda 3 ne kaɗai aka bayyana sunayen waɗanda aka ba kwangilar da kuma adadin kuɗaɗen da za a kashe.

Waɗanda ba a bayyana sunayen masu kwangila da na kamfanonin da aka baiwa ba, sun haɗa da: Aikin sa na’urori a Filin Jirgin Saman Murtala Mohammed da ke Legas.

Akwai kuma aikin shimfiɗa wayoyin intanet domin ƙara ƙarfin intanet a Najeriya.

Akwai aikin kwangila a Hukumar NITDA da sauran su.

1. Shirin ƙaddamar da ayyukan raya ƙasa da Gidaje na Haɗin-gwiwa (PPP).

2. An jaddda cewa duk wanda ya je Filayen Jiragen Gwamnatin Tarayya sai ya biya haraji kafin ya shiga. Har Shugaban Ƙasa da Mataimakin sa sai sun biya haraji kafin su wuce.

3. An haramta ginar yashi ko rairayi ko ƙasa daga tazarar da ba ta kai nisan kilomita 10 da gadar Gwamnatin Tarayya ba.

4. Gwamnatin Tarayya ta bada wa’adin makonni huɗu a sauya fasalin bayar da bizar gaggauta bai wa baƙi masu kawo ziyara da harkokin kasuwanci damar shigowa Najeriya.

5. Za a gina tashoshin hawa da sauka motocin haya a Kugbo, Abuja Central Area da Mabushi duk a FCT, kan kuɗi Naira biliyan 51, a cikin watanni 15.

6. Za a gina Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja, kan kuɗi Naira biliyan 37.2.

7. An amince Hukumar Kwastan ta sayo motoci Toyota Land Cruiser Buffalo guda 200, kan kuɗi Naira biliyan 12.5. Kuma su kasance ba masu amfani da fetur ba.

8. An amince a cire Naira tiriliyan 1.6 domin fara aikin titin Legas zuwa Kalaba.

9. An amince da bada kwangilar gyaran titin Koton-Ƙarfe zuwa Abaji, kan titin Abuja zuwa Lokoja, kan kuɗi Naira biliyan 89.

20. An bada kwangilar gina titin by-pass a Kano, kan kuɗi Naira biliyan 230. Aikin mai tsawon kilomita 37, zai ƙunshi har da gina gadoji da gadojin sama masu yawa.

11. An amince da kwangilar aikin titin Sokoto-Illela-Badagry. Wanda ake sa ran zai haɗe da titin Legas zuwa Kalaba.

People are also reading