Jam'iyyar PDP Ta Gayawa Tinubu Gaskiyar Halin da Ake Ciki a Kasa, Ta Ba Shi Shawara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishɗi
FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta zargi jam’iyyar APC da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da jefa ƴan Najeriya cikin tsabagen wahala da talauci.
Jam'iyyar adawan ta bayyana cewa ƴan Najeriya sun fusata kan halin da ƙasar nan ke ciki.
PDP ta caccaki jam'iyyar APC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam’iyyar PDP ta kuma ce jam’iyyar APC ta tozarta tsarin dimokuradiyya wanda marigayi Cif MKO Abiola ya yi fafutuka a kai, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Jam’iyyar PDP ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Debo Ologunagba, ya fitar, rahoton The Punch ya tabbatar.
PDP ta bukaci ƴan Najeriya da su yi amfani da bikin ranar dimokuradiyya na bana wajen nuna adawa da tsare-tsaren APC waɗanda suka jefa mutane cikin wahala.
"Abin takaici ne ƙasarmu na bikin ranar dimokuraɗiyya a ƙarƙashin gwamnatin da ta yi fice wajen maguɗin zaɓe, keta kundin tsarin mulki, tauye ƴan adawa domin mayar da Najeriya ƙarƙashin jam'iyya ɗaya."
"Abu mafi takaici shi ne dukkanin ci gaban da gwamnatocin PDP suka samu wajen bunƙasa dimokuraɗiyya a Najeriya, gwamnatocin APC sun share su."
- Debo Olugunagba
Jam'iyyar PDP ta buƙaci shugaban ƙasan da ya yi amfani da wannan lokacin wajen yin tunani kan halin da ƙasar nan ke ciki a a ƙarƙashin mulkinsa duba da yadda ake ta ƙorafi kan yunwa da tsadar rayuwa a ƙasar.
PDP ta tunatar da shugaban ƙasan cewa akwai talauci a ƙasa kuma ya kamata ya saurari ƴan Najeriya domin sake tsare-tsarensa waɗanda suka jefa mutane cikin wahala.
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya ɗora alhakin halin ƙuncin da ƴan Najeriya suke ciki kan jam’iyyar APC.
Tsohon mataimakim shugaban ƙasan ya kuma soki jam'iyyun adawa kan yadda suka haɗewa waje ɗaya domin kawo ƙarshen mulkin APC a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng