An Miƙa Wa Bola Tinubu Sunan Wanda Ya Kamata Ya Naɗa a Matsayin Ministan Jin Ƙai
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos- Masu buƙata ta nusamman a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta shiyyar Kudu maso Yamma, sun yi kira ga Bola Tinubu ya nada sabon ministan jin kai.
Naƙasassun sun miƙa wannan bukata ne a lokacin da suka kai ziyarar Barka da Sallah ga Shugaban Ƙasa Tinubu a jihar Legas.
Sun bai wa shugaban ƙasar shawarin ya ɗauko Dokta Adenike Tejuoso ya naɗa shi a matsayin sabon ministan harkokin jin kai da yaye talatauci, The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙungiyar nakasassun APC na shiyyar, Abayomi Soetan, ya ce Tejuoso ya fi kusanci da mutanen da ke da bukatu na musamman da sauran rukunin mabuƙata.
Ya bayyana Tejuoso a matsayin abin koyi da ya ba da gudunmawa mai tarin wajen ci gaban al’umma da kasa baki ɗaya
Soetan ya kara da cewa Tejuoso ya tallafawa marasa galihu a lokuta da dama, bisa haka suke ganin shi ya fi cancanta da kujerar ministan jin ƙai.
Ya kuma buƙaci ‘yan Najeriya da su marawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu baya duk da kalubalen da ake fuskanta na tattalin arziki wanda ya kawo tsadar rayuwa.
Mista Soetan ya roƙi ƴan Najeriya kar su gaji kuma su ci gaba da nuna juri, inda ya ƙara da cewa duka wannan wahalhalun da ake ciki za su zama tarihi nan gaba.
Idan baku ma ba shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya dakatar da ministar jin kai da yaye talauci, Dokta Betta Edu, bisa zarginta ɗa hannu a badaƙalar wasu kuɗi.
A wani rahoton kun ji cewa APC ta yi kira ga Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci domin kawo karshen kashe-kashen rayuka a jihar Ribas.
Shugaban APC na rikon kwarya a jihar, Tony Okocha ne ya yi wannan kira jim kaɗan bayan Gwamna Fubara ya rantsar da sababbin ciyamomi
Asali: Legit.ng