Home Back

‘Yancin Kananan Hukumomi: Kotun Koli Ta Bai Wa Jihohi 36 Kwana 7 Su Kare Kansu

leadership.ng 2024/7/1
Shari’ar Zaben Gwamnoni: Kallo Ya Koma Kotun Koli

Kotun kolin Nijeriya ta umarci gwamnonin jihohin kasar nan 36, da su kare kansu cikin kwanaki bakwai kan karar da gwamnatin tarayya ta shigar na neman cikkaken cin gashin kai ga kananan hukumomi 774 na kasar nan. 

Kotun kolin ta kuma umarci Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a bayan ya samu kariya daga gwamnonin, ya gabatar da amsarsa cikin kwanaki biyu.

Mai shari’a Garba Lawal, ya bayar da wannan umarni ne a ranar Alhamis yayin da yake yanke hukunci kan bukatar rage wa’adin da Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ya yi.

Mai shari’a Lawal, wanda ya jagoranci kwamitin mutane bakwai na kotun koli, ya ce hukuncin kotun ya ta’allaka ne kan gaggawar karar da kasa baki daya da kuma rashin kin amincewa da lauyoyin gwamnatin jihohi 36 na tarayya.

Kotun kolin ta ce dole ne a kammala gabatar da dukkan matakai da musayar bayanai da suka kamata a kan lokaci, inda ta sanya ranar 13 ga watan Yuni dan sauraron karar.

Mai shari’a Lawal ya bayar da umarnin aika sabuwar sanarwar sauraron karar ga jihohi takwas da ba su halarci shari’ar ba a ranar Alhamis ba, wanda suka hada da Borno da Kano da Kogi da Neja da Ogun da Osun da Oyo da kuma Sokoto, kasancewar lauyoyinsu ba su halarci kotun ba, duk da cewa an aike musu sakon zaman kotun.

People are also reading