"Ganduje Ya Lalata Sarautar Kano", Jigon APC Ya Faɗi Abin da Zai Faru da Jam'iyyar a Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC a Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya magantu kan rikicin sarautar Kano.
Lukman ya soki Gwamnatin Tarayya game da shiga rikicin sarautar jihar bayan tuge sarki na 15, Aminu Ado Bayero.
Jigon APC ya ce shigar gwamnatin Bola Tinubu wannan harka da lalata lamuran kasar zai kawo cikas ga jam'iyyar a yankin Arewa a 2027, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce babban kuskure ne a siyasa Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da jami'an tsaro domin neman kawo cikas a matakin gwamnatin jihar Kano, Daily Post ta tattaro.
"A matsayina na ɗan APC a Arewa maso Yamma abin takaici ne yadda Gwamnatin Tarayya ta shiga lamarin sarautar jihar Kano."
"Dalilin matakin tube sarakunan shi ne gyara barnar da Abdullahi Ganduje ya yi a jihar lokacin da yake mulkin Kano."
"Ya kamata Tinubu ya sani APC ta fadi a zabe ne saboda yadda Ganduje ya gudanar da mulkinsa a jihar."
- Salihu Lukman
Ya ce abin da Ganduje ya yi ya kara siyasantar da masarautu wanda a yanzu za su dawo wa'adi kamar yadda gwamnoni ke yi.
Lukman ya kara da cewa a yanzu farin jinin APC ya yi kasa a jihar Kano mama Arewa baki daya musamman irin matakan APC ke dauka a kasar.
Kun ji cewa mutane sun shiga fargaba bayan jiyo harbe-harbe a fadar Nasarawa da Aminu Ado Bayero yake.
Hakan ya biyo bayan umarnin kotu na tuge Aminu Ado karfi da yaji daga fadar bayan tube shi a sarauta.
Asali: Legit.ng