Ana Shirin Fita Zanga Zanga, Matasa Sun Farmaki Mota Makare da Kayan Abinci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Cross River - Miyagu akalla 100 ne suka farmaki motar bas dauke da kayan tallafi a jihar Cross River.
Bus din makare take da kayan abinci na kungiyar ƴan jaridu a jihar da ta nufi sakatariyar kungiyar.
Vanguard ta tattaro cewa matasan sun yi nasarar kwashe wasu daga cikin kayayyakin abinci bayan fasa tagogin motar a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daraktan yada labarai na hukumar agajin gaggawa ta NEMA a jihar, James Anam shi ya tabbatar da haka ga manema labarai.
Direba motar mai suna Joseph Akpaenin da kyar ya sha da rayuwarsa inda ya ce an dauke masa wayar salula yayin farmakin, Daily Post ta tattaro.
Akpaenin ya ce miyagun sun cigaba da kwashe kayan abincin da ke zuba daga motar inda a lokacin ne ya samu ya tsira da rayuwarsa.
Da yawa daga cikin wadanda suke tawagar sun samu raunuka cikin har da dan jarida daga Tribune inda suke kwance a gadon asibiti.
Kun ji cewa Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya tabbatar da cewa ya biya mafi yawan bukatun matasa masu shirin zanga-zanga.
Tinubu ya ce ya dauki wasu matakai masu muhimmanci wadanda za su kawo dauki ga al'umma baki daya duba da halin da ake ciki.
Wannan na zuwa ne yayin da matasa ke shirin fita zanga-zanga a kasar musamman saboda halin kunci da kuma tsadar rayuwa.
Asali: Legit.ng