Rikici Ya Barke Bayan Gwamna Ya Kori Shugabannin Kananan Hukumomi, Sun Ja Daga
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara ya rusa duka shugabannin kananan hukumomi 23 a jiharsa.
Fubara ya dauki wannan matakin ne bayan wa'adinsu ya kare a watan Yunin 2024 da muke ciki a jihar.
Gwamnan ya umarci su mika dukan komai da ke hannunsu ga shugabannin gudanarwa na kananan hukumomisu, cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ina son yin amfani da wannan dama wurin godewa duka shugabannin kananan hukumomi da kansiloli kan kokarinsu a Rivers."
"A madadin gwamnati da al'ummar jihar Rivers muna yi muku godiya bayan wa'adinku ya kare a jiya 17 ga watan Yuni."
"Ina umartan duka shugabannin gudanarwa na kananan hukumomi su karbi ragamar shugabancin karamar hukumar da suke wakilta."
- Siminalayi Fubara
Wannan na zuwa ne bayan rikita-rikita a aka yi ta yi kan wa'adin shugabancin kananan hukumomi a jihar.
Mafi yawan shugabannin kananan hukumomin suna tare da Ministan Abuja, Nyesom Wike tun yana mulkin jihar.
Da dama daga cikinsu sun kalubalanci karewar wa'adin nasu inda suke barazana ga duk wanda ya ke shirin korarsu.
Shugaban karamar hukumar Eleme, Obarilomate Ollor ya gargadi masu kokarin korarsa daga ofishinsa inda ya ce kada wani ya kuskura ya zo kusa da shi.
Har ila yau, an jibge jami'an tsaro kananan hukumomin Port Harcourt da Obio/Akpor saboda gudun barkewar rikici.
Bayan karewar wa'adin, matasa sun mamaye hedikwatar kananan hukumomin Degema da kuma Asari-Toru.
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya soki gwamnatin Nyesom Wike kan rashin katabus a jihar.
Fubara ya ce ayyukan da ya yiwa al'ummar jihar Rivers ya fi shekaru takwas na gwamnatoci da dama da aka yi a jihar baki daya.
Asali: Legit.ng