Home Back

Innalillahi: Wani Alhaji Dan Najeriya Ya Sake Rasuwa a Saudiyya

legit.ng 2024/7/2
  • Wani daga cikin Alhazan Najeriya da ke ƙasa mai tsarki wajen gudanar da aikin Hajjin bana ya riga mu gidan gaskiya
  • Alhajin wanda ba a bayyana sunansa ko jihar da ya fito ba ya yanke jiki ya rasu ne lokacin da yake kan hanyar zuwa wurin jifar shaidan
  • Hukumomi a Saudiyya sun sanya dokar hana zuwa wajen jifar shaidan daga ƙarfe 11:00 na safe zuwa ƙarfe 4:00 na yamma saboda zafin da ake fama da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Saudiyya - Wani Alhaji ɗan Najeriya da ke ƙasar Saudiyya ya faɗi ya mutu yayin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024.

Alhajin ya rasu ne a kan hanyarsa ta zuwa Jamarat domin gudanar da ibadar jifar shaidan.

Alhaji dan Najeriya ya rasu a Saudiyya
Alhaji dan Najeriya ya rasu a Saudiyya Hoto: Haramain Sharifain Asali: Facebook

Shugaban tawagar likitocin Najeriya mai kula da aikin hajjin 2024, Dakta Abubakar Adamu, ya tabbatar da hakan a wata hira da manema labarai, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saudiyya ta sanya doka

Ma'aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta sanar da dakatar da mahajjata zuwa gadar Jamarat daga ƙarfe 11:00 na safe zuwa ƙarfe 4:00 na yamma, domin gudanar da ibadar saboda tsananin zafi.

An gargaɗi Alhazan da su guji ƙin bin umarnin da ya haramta musu yin jifa a cikin lokacin da aka ƙayyade.

Likitoci sun wayar da kan Alhazai

Dakta Abubakar Adamu ya ce tun kafin a fara aikin Hajjin, ya wayar da kan ƴan tawagar likitocin hanyoyin da za su bi domin kare kansu daga zafin da ka iya tasowa saboda rana, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

Ya shawarci Alhazai da su yi amfani da laima domin kare kansu daga zafin rana.

Likitan ya kuma yi kira ga Alhazai da su riƙa neman inuwa a duk lokacin da hakan zai yiwu domin gujewa hasken rana, kuma su riƙa shan ruwa a kowane lokaci ko da ba su jin ƙishi.

Mataimakiyar daraktan hulɗa da jama’a ta NAHCON, Fatima Usara, ta ce hukumar ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen wayar da kan Alhazai kan illolin da ke tattare da barin kansu cikin rana.

Wata Hajiya ta rasu a Saudiyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa Allah ya yi wa wata mahajjaciya daga jihar Kaduna, Hajiya Asma’u Muhammad-Ladan rasuwa a kasa mai tsarki.

Hajiya Asma'u ta rasu ne a asibitin King Fahad da ke birnin Makkah a Saudi Arabia ranar Jumu'a, 14 ga watan Yuni bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

People are also reading