Katsina: Gwamna Ya Ba Ma’aikata Goron Sallah N45,000, Ya Gindaya Sharuda
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Katsina – Gwamna Umaru Dikko Radda na jihar Katsina ya gwangwaje ma’aikata da barka da sallah a jihar.
Radda ya ba da kyautar N15,000 ga duka ma’aikatan jihar yayin da kuma ya ba su bashin N30,000 domin gudanar da salla cikin walwala.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na X a yau Asabar 8 ga watan Yuni.
Gwamnan ya ce ya dauki wannan matakin ne domin ragewa ma’aikatan jihar halin da ake ciki a fadin kasar.
“Ganin yadda babbar sallah ke karatowa, na dauki matakin tallafawa ma’aikata wurin ba su bashin N45,000 hade da goron sallah.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Domin saukaka musu biyan kudin cikin sauki, za a cire N10,000 kowane wata har N30,000 a watannin Yuli da Agusta da kuma Satumba.”
“Sannan na ba duka ma’aikatan jihar kyautar N15,000 domin gudanar da bukuwan sallah cikin walwala.”
Dikko Umaru Radda
Karin bayani na tafe...
Asali: Legit.ng