Home Back

"Kudin Sun Shigo, Ya Za a Yi": Shehu Sani Ya Faɗi Yadda Za Ta Kaya Bayan Ƴancin Ƙananan Hukumomi

legit.ng 2024/8/25
  • Yayin da Kotun Koli ta yi hukunci kan ƴancin ƙananan hukumomi a Najeriya, Sanata Shehu Sani ya yi martani kan lamarin
  • Sanatan ya ce kusan gidan jiya ne tun da wasu daga ciyamomin sai sun nemi izinin yadda za su kashe kudaden idan aka tura musu
  • Martanin Shehu Sani na zuwa ne bayan umarnin da Kotun Koli ta ba Gwamnatin Tarayya ta rika biyan ƙananan hukumomi daga asusunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yi martani bayan hukuncin kotu kan kananan hukumomi.

Sanatan ya ce hukuncin aikin banza ne saboda yadda shugabannin ƙananan hukumomin za su yi ga gwamnonin jihohinsu.

Shehu Sani ya magantu kan ƴancin kananan hukumomi
Sanata Shehu Sani ya fadi yadda shugabannin ƙananan hukumomi za su yiwa gwamnoni. Hoto: Shehu Sani. Asali: Facebook

Kananan hukumomi: Shehu Sani ya magantu

Tsohon sanatan ya bayyana haka ne a yau Alhamis 11 ga watan Yulin 2024 a shafinsa na X jim kadan bayan hukuncin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sani ya ce duk lokacin da kudin karamar hukuma ya shigo, ciyaman sai ya nemi izinin yadda zai yi da kuɗin a wurin gwamna.

"Mai girma gwamna, kudin nan sun shigo mene ya kamata a yi da su?"
"Duk da hukuncin Kotun Koli, mafi yawan shugabannin kananan hukumomi haka za su yi lokacin da kudinsu suka shigo daga sama."

- Shehu Sani

Sanatan ya yi martanin ne yayin da ake ta murna bayan hukuncin Kotun Koli kan shari'ar Gwamnatin Tarayya da gwamnoni 36.

A yau Alhamis 11 ga watan Yulin 2024, kotun ta raba gardama kan rigimar inda ta kalubalanci gwamnonin kan rike kudaden kananan hukumomi.

Kotun ta umarci Gwamnatin Tarayya ta fara biyan ƙananan hukumomi daga asusunta kamar yadda take yiwa jihohi.

Wannan mataki ya biyo bayan shigar da korafi kan gwamnonin da Gwamnatin Tarayya ta yi game da ƴancin ƙananan hukumomi.

Shugaban karamar hukuma ya naɗa hadiman 100

A wani labarin, kun ji da wani shugaban karamar hukuma a jihar Rivers ya nada hadimai na musamman guda 100.

Hon. Chijioke Ihunwo da ke jagorantar karamar hukumar Obio-Akpor shi ya dauki wannan mataki domin inganta shugabancinsa.

Asali: Legit.ng

People are also reading