Home Back

Tsadar Rayuwa: Kwanaki Bayan Samun Mukami, Tsohon Gwamna Ya Kare Tinubu

legit.ng 2024/6/26
  • Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda ya wanke shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kuncin rayuwa da ake ciki
  • Malam Isa Yuguda ya ce shugaban kasar shima a haka ya samu kasar cikin rudanin tattalin arziki da rashin daidaiton al'amura
  • Har ila yau ya kuma bayyana yadda cire tallafin man fetur ya jawo amfani ga Najeriya maimakon yadda wasu ke sukan matakin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda ya wanke shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan matsin rayuwa da Najeriya ke ciki.

Isa yuguda
Isa Yuguda ya ce bai kamata a zargi Tinubu kan wahalar rayuwa ba. Hoto: Isa Yuguda Asali: Facebook

Malam Isa Yuguda ya ce bai kamata a zargi shugaba Tinubu kan jawo tashin farashin kayyakki da sauran wahalhalun da yan Najeriya ke fama da su ba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa tsohon gwamnan ya yi maganganun ne wajen wani taro da tsagin jam'iyyar APC ya shirya a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wa ya jawo wahalhalu a Najeriya?

Duk da wahalhalun rayuwa da yan Najeriya suka shiga a mulkin Tinubu, Malam Isa Yuguda ya ce shugaban kasar shima gadonsu ya yi.

Ya ce tattalin arzikin kasar ya tabarbare tun kafin zuwan shugaba Bola Tinubu saboda haka bai kamata a zarge shi ba.

Kokarin Tinubu wajen kawo gyara

Malam Isa Yuguda ya kara da cewa shugaba Bola Tinubu ya dauki matakan da suka dace wajen kawo cigaban tattalin Najeriya.

Ya ce ba don Tinubu ya dauki matakin cire tallafin man fetur da Naira ba, da yanzu kasar ta kai ga durkushewa.

Tinubu ya kyauta kan cire tallafin mai

Tsohon gwamnan ya ce duk da cewa ba Tinubu ba ne ya fara cire tallafi man fetur amma hakan ya jawo amfani ga Najeriya.

Ya ce man da ake amfani da shi a Najeriya ya ragu sosai saboda cire tallafi ya sa an daina satar man zuwa karshen ketare.

A cewar Isa Yuguda, a yanzu man da ake amfani da shi a Najeriya ya ragu da kashi 50% saboda an daina satar shi zuwa kasashen ketare.

Tinubu ya raba abinci

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aika tarin kayan abinci ga gwamnatin jihar Zamfara a jiya Litinin, 20 ga watan Mayu.

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya tabbatar da karbar kayan abincin tare da bayyana adadinsa da yadda za su raba shi.

Asali: Legit.ng

People are also reading