Home Back

SHARI’AR ZARGIN TA’ADDANCI: Kotu ta hana belin Shugaban Miyetti Allah, Bello Boɗejo

premiumtimesng.com 2024/5/19
SHARI’AR ZARGIN TA’ADDANCI: Kotu ta hana belin Shugaban Miyetti Allah, Bello Boɗejo

Shugaban Ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Boɗejo, ya nemi a bada belin sa a Babbar Kotun da ke Abuja.

Boɗejo dai ya na tsare ne a magarƙamar Hukumar Leƙen Asiri ta Sojoji (DIA), a Abuja, kuma ana tuhumar sa da laifin ta’addanci.

Gwamnatin Najeriya na zargin sa da kafa ƙungiya ta zaratan Fulani tsantsa, ba bisa ƙa’ida ba. Sunan ta Ƙungiyar Zaman Lafiya.

Wace Ce Ƙungiyar Zaman Lafiya?:

Bello Boɗejo ya kafa Ƙungiyar Zaman Lafiya a garin Lafiya, babban birnin Jihar Nassarawa. Kuma shi ma a Karu kusa da Abuja Hedikwatar sa ta Miyetti Allah Kautal Hore ta ke. Karu ƙarƙashin Jihar Nasarawa ne, amma garin ya na kusa da Abuja.

An gurfanar da Boɗejo kotu tare da zargin sa da laifuka uku, waɗanda Antoni Janar na Tarayya ya gurfanar da shi kan zargin Karya Dokar Ta’addanci ta 2022.

Sai dai kuma Boɗejo ya ƙaryata dukkan zarge-zargen da ake yi masa.

Yadda Boɗejo Ya Nemi Beli, Kotu Ta Hana:

Yayin zaman kotun na ranar Talata, Bello Boɗejo ta hannun lauyan sa, kuma babban lauya Ahmed Raji, ya nemi a bada beli.

Lauya Raji ya ce ya dace a bada belin Boɗejo, sai a ci gaba da shari’a.”

Lauya Raji ya ce kotu na da hurumin bada belin Boɗejo, wanda ke tsare tun a ranar 27 ga Janairu, 2024, domin zarge-zargen da ake masa ba su wuce hurumin beli ba.

Sannan kuma ya ce Bello Boɗejo na fama da matsananciyar rashin lafiya.”

Ya ce har yau wanda yake karewa ɗin idan aka dubi Sashe na 36 na Kundin Dokokin Najeriya, zargi ne har yanzu ake masa, ba a tabbatar da laifin a kan sa ba.

Sai dai kuma lauya mai shigar da ƙara, Y.A Imana, ya roƙi kotu kada ta bada belin Boɗejo, ya ce akwai hatsari ga sha’anin tsaron ƙasa idan aka bada belin sa.

Daga nan Mai Shari’a ya ɗage zaman sai ranar 30 ga Mayu, domin ya yanke hukuncin beli ko hana beli.

‘An Hana Lauya Da Makusantan Bello Boɗejo Ganawa Da Shi’ – Ƙanen Sa, Mohammed Musa:

A cikin wata takardar rantsuwar da ke ƙunshe da ƙorafi, ɗan’uwan Bello Boɗejo mai suna Mohammed Musa, ya bayyana wa kotu a rubuce cewa shugaban na Miyetti Allah Kautal Hore da ke tsare hannun sojoji tun ranar 23 ga Janairu, “an hana shi ganawa da lauyoyin sa, iyali, abokai da makusantan sa.”

Musa ya ce Boɗejo mutumin kirki ne, mai kishin Najeriya. Ya ce ya kafa ƙungiyar bijilante ne domin kawo tsaro a cikin al’umma, ba domin aikata wasu ayyukan ta’addanci ba.

Gwamnatin Najeriya Ba Ta Son Kotu Ta Bayar Da Belin Bello Boɗejo:

Gwamnatin Najeriya ba ta goyon bayan a bayar da belin Bello Boɗejo, inda ta ce duk irin tsananin ciwo ko rashin lafiyar da ke damun sa, akwai ƙwararrun likitoci a Cibiyar Duba Marasa Lafiya da ke DIA.

Gwamnati ta ƙara da cewa kuma Ofishin DIA ya na kusa da Asibitin Fadar Shugaban Ƙasa, a Abuja, wanda “babu wurin da ya fi shi ƙwararrun likitoci da masu duba marasa lafiya.”

Gwamnati ta zargi Boɗejo da laifin kafa ƙungiya ta zaratan Fulani zalla a Jihar Nasarawa, ba tare da neman izni daga Hukumomin Tsaro na Tarayya ba.

Gwamnatin Tarayya na kuma zargin Boɗejo da ɗaukar ɗaukar nauyi da kuma shiga cikin sha’anin da ke da nasaba ko kusanci da ayyukan barazana ga tsaron ƙasa da rayukan al’umma.

Gwamnatin Tarayya ta ce irin ayyukan da Boɗejo ke yi na bayar da kayan aiki, tallafi da kuɗaɗen zirga-zirga domin tafiyar da ayyukan, lamarin da ya saɓa tare da karya dokokin Najeriya Sashe na 29, 2(3)(g)(xii) da 12(a) da Sashe na 2(3)(g)(xii), da 13(2)(b) na Dokokin Haramta Ayyukan Ta’addanci na 2022.

People are also reading