Zamfara: Ana Kukan Babu Kudi, Gwamnati Ta Fara Aikin Filin Jirgin Saman N62bn
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Zamfara- Ministan harkokin sufurin jirgin sama, Festus Keyamo ya dora harsashin fara aikin katafaren jirgin sama a Zamfara da rashin tsaro ya dabaibaye a wani yunkuri da bunkasa jihar.
Filin jirgin na kasa da kasa da za a gina a Gusau zai lashe N62.8bn, kuma ana sa ran zai bunkasa tattalin arziki musamman a bangarorin noma, ilimi da yawon bude idanu.
A sakon da Gwamna Dauda Lawal Dare ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce idan filin jirgin ya kammala, jihar Zamfara za ta kara daukaka a idon duniya ta fuskar kasuwanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Festus Keyamo ya bayyana aikin katafaren filin jirgin sama da aka kaddamar a jihar Zamfara da cewa zai cicciba jihar ta bangarori da dama.
Vanguard News ta wallafa Ministan na cewa ;
“ Ina fadin cewa a yankin Arewa maso Yamma, jihar Zamfara ba ta samun irin wadannan manyan ayyukan ci gaba.
Sauran sassan na da filayen jirgin sama masu kyau, mutanen da ke zaune a yankin na iya amfani da su, amma ita Zamfara an bar ta a baya.”
A jawabinsa, gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya yi alkawarin za a kammala aikin jirgin saman cikin watanni 30.
A baya mun kawo labarin cewa gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Dare ya karrama askawaran jihar da suke kokarin kawar da rashin tsaro a sassan jihar
Askarawa 20 gwamnan ya karrama da ya ce suna taka rawa wajen dakile ta'addancin da ya addabi sassan Zamfara, sannan ya yi alkawarin taimakawa iyalan wadanda suka rasu.
Asali: Legit.ng