Home Back

Isra'ila ta ce babu batun tsagaita wuta a Zirin Gaza

dw.com 2024/6/29
Israels Ministerpräsident Netanjahu
Hoto: Ohad Zwigenberg/AP/dpa/picture alliance

Furucin nasa na wannan Asabar tuni ya haifar da shakku kan yiwuwar aiki da sabon yunkurin tsagaita wuta da shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar a ranar Juma'a da ta gabata. 

A yayin da yake gabatar da kudurin, shugaban na Amurka ya ce da farko sabuwar tattaunawar na bukatar tsagaita wuta na makonni shida, inda Isra'ila za ta janye sojojinta daga yankunan da ke da mutane a Zirin Gaza.

Ya ce hakan zai bayar da dama ga Falasdinawan da suka rasa muhallansu su koma gida yayin da ita kuma kungiyar Hamas ake bukatar ta saki 'yan Isra'ila da take rike da su domin bude kofar sakin Falasdinawan da ke tsare a gidajen yarin Isra'ila.

Majalisar Dinkin Duniya da kasashen kungiyar Tarayyar Turai ciki har da Jamus sun nuna amincewarsu ga sabuwar tattaunawar sulhun da ake sa ran zango na biyu zai samar da tsagaita wuta ta din-din a yankin na Zirin Gaza. Sai dai furucin firaministan Isra'ila na kokarin ganin bayan kungiyar Hamas ka iya kawo cikas ga shirin.
 

People are also reading