Home Back

Gwamnantin Zamfara Ta Fara Biyan Albashi Watan Yuni Domin Hidimar Sallah

leadership.ng 2024/7/2
Gwamnantin Zamfara Ta Fara Biyan Albashi Watan Yuni Domin Hidimar Sallah

Daga Hussaini Yero Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya tabbatar da fara biyan sabon tsarin Albashi na Naira dubu Talatin daga dubu Shida a Yau na wannan watan da muke ciki dan ma’aikata suyi hidar Sallah cikin wallah.

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana haka ne a wajan taron Ranar demakwaradiya ayau a filin dandalin ‘yanci da ke tsakiyar garin Gusau , Babban Birnin Jihar Zamfara.

“A Jawabin nasa gwamna Dauda ya dau alwashin inganta Jindadin ma’aikata wanda abun takaicin ne tsawon sheru da Gwamnonin da akayi suka wuce a Zamfara sun gaza biyan ma’aikata Tsarin Albashi mafi Karancin na dubu Talatin sai na dubu Shida wannan abuntakaici inji gwamna Dauda.

Akan haka ne ya tabbatar da cewa,yau cikin darennan Insha Allah kowane Ma’aikaci zaiji Albashi sa na wannan wata kuma sabon tsari inji gwamna Dauda.

People are also reading