Home Back

Wata Miyar: Tsadar Rayuwa Ta Sanya Shugaban Liberia Zaftarewa Kansa Albashi

legit.ng 2024/8/25
  • Shugaban kasar Liberia, Joseph Boakai ya ragewa kansa albashi biyo bayan matsin rayuwa da yan kasar ke kokawa a kai
  • Fadar shugaban kasar na ganin wannan ya nuna damuwar gwamnati kan matsalar da jama'ar kasar ke ciki
  • Shugaba Joseph Boakai ya rage albashinsa da 40%, wanda ke nufin yanzu zai rika karbar albashin $8,000 a wata

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Liberia- Biyo bayan koken jama'ar Liberia kan matsin tattalin arziki, shugaban kasar, Joseph Boakai ya ragewa kansa albashi. Shugaba Boakai ya bayyana cewa zai zaftare 40% na albashinsa domin damuwa da halin da mutanensa ke ciki na matsin tattalin arziki da tashin farashi.

Joseph
Shugaban kasar Liberia, Joseph Boakai ya rage albashinsa da 40% Hoto: Seyylou Asali: Getty Images

BBC News ta wallafa cewa ana ta cece-kuce kan albashin jami'an gwamnati saboda yadda rayuwa ta yi tsada a kasar.

Shugaba Boakai ya rage albashinsa da 40%

Shugaban kasar Liberia, Joseph Boakai ya bayyana rage albashinsa da 40%, bayan 'yan kasarsa sun koka kan matsin rayuwa. Wannan na nufin albashinsa zai koma $8,000 daga $13,400 da ya ce gwamnati na biyansa a watan Fabrairu. Channels Television ta wallafa cewa haka kuma shugaban kasar ya dauki alkawarin daidaita albashin ma'aikata yadda zai zo dai-dai da halin da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fadar shugaban kasar ta Liberia na ganin matakin ya nuna irin yadda gwamnatin Boakai ta damu da talakawan kasar da gudanar da mulki da adalci.

Ko a gwamnatin baya ta shugaba George Weah a Liberia, an rage albashin shugaban kasa da 25%.

Gwamnonin Najeriya sun yi zauna kan albashi

A baya kun ji cewa gwamnonin Najeriya sun bayyana cewa ba za su iya biyan albashi ba idan aka nemi kari ga ma'aikata.

Kungiyar gwamnonin kasar nan ta cikin sanarwar da ta fitar ta bayyana damuwa kan kokarin gwamnatin tarayya na kara albashi zuwa N62,000.

Kungiyoyin kwadago a Najeriya na neman gwamnati ta kara mafi karancin albashi daga N30,000 zuwa N615,000, daga bisani aka sauko zuwa N250,000.

Asali: Legit.ng

People are also reading