Home Back

Yajin Aiki: NLC Ta Fitar da Sanarwa Kan Makomar Yajin Aiki a Yau Talata, Ta Yi Gargadi

legit.ng 2024/6/29
  • Kungiyar kwadago a Najeriya (NLC) ta fitar da sanarwa da safiyar yau Talata 4 ga watan Yuni kan ci gaba da yajin aiki
  • Kungiyar ta tabbatar da cewa za a ci gaba da yajin aiki har sai bayan tattaunawa da za ta yi da gwamnati a yau Talata
  • Wannan na zuwa bayan ganawar da ta yi da Gwamnatin Tarayya a jiya Litinin 3 ga watan Yuni kan yajin aikin da aka fara yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar kwadago ta NLC ta magantu bayan tattaunawar da ta yi gwamnati kan yajin aiki a Najeriya.

Kungiyar ta ce a yau za a ci gaba da yajin aiki har sai an ji daga gare ta bayan ganawa da suka yi da Gwamnatin Tarayya.

NLC ta bayyana haka ne da safiyar yau Talata 4 ga watan Yuni a shafinta na X inda ta ce a ci gaba da zama a gida.

Duk da zaman da aka yi a jiya Litinin 3 ga watan Yuni da gwamnati, kungiyar ta ce za ta yi duba kan yarjejeniyar da aka yi a ganawar a jiya Litinin.

Kungiyar ta bukaci ci gaba da yajin aikin har sai ta fitar sanarwa bayan ganawa a yau Talata 4 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Har sai kun ji daga gare mu a ganawar da za mu yi a yau Talata 4 ga watan Yuni, za a ci gaba da yajin aiki."

- NLC

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading