Yajin Aiki: NLC Ta Fitar da Sanarwa Kan Makomar Yajin Aiki a Yau Talata, Ta Yi Gargadi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kungiyar kwadago ta NLC ta magantu bayan tattaunawar da ta yi gwamnati kan yajin aiki a Najeriya.
Kungiyar ta ce a yau za a ci gaba da yajin aiki har sai an ji daga gare ta bayan ganawa da suka yi da Gwamnatin Tarayya.
NLC ta bayyana haka ne da safiyar yau Talata 4 ga watan Yuni a shafinta na X inda ta ce a ci gaba da zama a gida.
Duk da zaman da aka yi a jiya Litinin 3 ga watan Yuni da gwamnati, kungiyar ta ce za ta yi duba kan yarjejeniyar da aka yi a ganawar a jiya Litinin.
Kungiyar ta bukaci ci gaba da yajin aikin har sai ta fitar sanarwa bayan ganawa a yau Talata 4 ga watan Yuni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Har sai kun ji daga gare mu a ganawar da za mu yi a yau Talata 4 ga watan Yuni, za a ci gaba da yajin aiki."
- NLC
Karin bayani na tafe....
Asali: Legit.ng