Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Tsaron Zamfara 3
Akalla jami’an tsaron Jihar Zamfara uku ne suka rasa rayukansu yayin da ‘yan bindiga suka yi musu kwanton bauna a unguwar Jambako da ke karamar hukumar Maradun a jihar.
Wani mutum a yankin mai suna, Sanusi Muhammad ya shaida wa wakilinmu cewa ‘yan bindigar sun yi wa jami’an CPG kwanton bauna a Tungar Nayarciga a kan hanyarsu ta zuwa garin Faru.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun kuma kwashe makamansu da baburansu.
Harin ya haifar da rudani da fargaba a tsakanin mazauna yankin.
Bayani na tafe…