Bayan Dala Ta Karye, Farashin Man Fetur Ya Ragu a Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kamfanin mai na Najeriya (NNPC Ltd) a ranar Laraba ya musanta rahotannin da ke yawo cewa cewa an samu raguwar farashin man fetur da man dizal.
NNPCL ya bayyana cewa rahotannin da ake yaɗawa cewa ya rage farashin man fetur da dizal a gidajen sayar da mai a fadin kasar nan ba gaskiya bane.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kamfanin ya fitar a shafinsa na manhajar X watau Twitter ranar Laraba, 27 ga watan Maris, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban sashin yaɗa labarai na NNPCl, Olufemi Soneye, wanda ya rattaba hannu kan sanarwar, ya ce rahotannin saukar farashin ba gaskiya bane.
Wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa ƴan kasuwa sun rage farashin mai daga N640 zuwa N630 yayin da kamfanin NNPC ke sayar da lita kan N570 a gidajen mai.
Amma da yake mayar da martani, kakakin NNPC, Mista Soneye ya ce rahotannin karya ne kuma ya bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da su gaba daya.
"Kamfanin NNPCL na son ya fayyace gaskiya game da jita-jitar da ke nuna cewa an rage farashin man fetur (PMS) da Automotive Gas Oil (dizal) a gidajen sayar da mai a fadin kasa.
“Kamfani ya tabbatar da cewa waɗannan rahotanni karya ne kuma ya bukaci ɗaukacin ‘yan Najeriya da su yi watsi da su gaba daya."
- In ji Olufemi Soneye.
Kamfanin NNPC Ltd ya jaddada kudirinsa na ci gaba da samar da wadataccen man fetur a duk gidajen sayar da mai a lungu da saƙo na Najeriya.
Ƴan kasuwar canji sun musanta rahoton da ke yawo cewa farashin Dala ya ƙara karyewa, ya koma N1,000 kan kowace $1.
Wannan na zuwa ne bayan wani rahoto ya karaɗe shafukan sada zumunta cewa Dala ta karye zuwa N1000 a Otal ɗin Sharaton da ke Zone 4 a Abuja.
Asali: Legit.ng